Shugaban ?asa Bola Tinubu ya ce a shirye gwamnatinsa take wajen mara wa babban kamfanin fasaha na Google baya don samar da ayyukan yi miliyan guda a ?asar.
Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da mataimakin shugaban kamfanin Mista Richard Gingras ya ziyarce shi a fadarsa da ke Abuja.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ?asar Dele Alake ya fitar, Shugaban na Najeriya ya ce Najeriya na da matasa masu basira da fasaha, wa?anda koyaushe a shirye suke wajen koyon sabbin abubuwa musamman a wannan zamani na bun?asar fasahar zamani.
Yana mai cewa kamfanin google na da dukkan abubuwan da matasan Najeriya ke bu?ata don bun?asa fasaharsu.
“Ina farin ciki cewa Google a shirye yake ya yi aiki da mu. kun amsa kiranmu wajen samar wa matasanmu sabbin ayyukan fasahar zamani. Kuna mara wa yun?urinmu baya na bun?asa sabbin hanyoyin tattalin arziki na zamani. A shiye muke mu yi aiki da ku kan yunkurinku na amar da ayyukan yi miliyan guda ga matasanmu”, in ji shugaban na Najeriya.
Ya ?ara da cewa “Za mu ba ku duk goyon bayan da kuke bu?ata domin cika wannan buri naku”.
Najeriya na da miliyoyin matasa marasa aikin yi a ?asar wadda ta fi kowacce yawan al’umma a nahiyar Afirka
