Za A Bu?e Iyakokin Najeriya Nan Bada Da?ewa Ba – Buhari

Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba zai bada umarnin bude kan iyakokin Najeriya.

Ya bayyana hakan ne ga gwamnonin Najeriya 36 a ganawar da yayi da su ranar Talata, 8 ga watan Disamba, 2020 a fadar Shugaban Kasa dake birnin tarayya Abuja.

Buhari ya ce ya rufe iyakokin ne domin hana fasa ?wabrin makamai da kwayoyi amma tun da yanzu makwabtan Najeriya sun hankalta, zai iya bude wa.

Shugaban kasar ya bayyana tattaunawarsa da gwamnonin a shafinsa na Tuwita. “A ganawa da gwamnoni yau nayi bayanin cewa an kulle iyakokin Najeriya na kasa ne domin lura da fasa kwabrin makamai da kwayoyi. Amma yanzu da sakon ya isa ga kunnawan makwabtanmu, muna tunanin budewa nan ba da dadewa ba.”

Tun da fari dai mun kawo muku rahoton cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri tare da dukkanin gwanonin jihohi 36.

Sun yi ganawar ne a fadar Shugaban kasa da ke Abuja a ranar Talata, 8 ga watan Disamba. Ganawar tasu na zuwa ne bayan kungiyar gwamnonin kasar sun gana a makon da ya gabata tare da Shugaban kasar kan halin da lamarin tsaro ke ciki.

Related posts

Leave a Comment