Za?en 2023: Kudu Ya Kamata Mulki Ya Koma – Shekarau

Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewar abin da yafi kamata shine a mayar da Mulki Kudancin Najeriya a shekarar 2023, wannan shine adalci kuma zai taimaka wajen karfafa mulkin dimokura?iyyar a Najeriya.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai cikin shirin Sunrise Daily.

A cewarsa, duk da cewa ba ya rubuce a kundin tsarin mulkin, “akwai fahimtar daidaito da kuma ba kowa daman kama ludayin don adalci.”

Yayin da aka tambayeshi kan kiran da yankin Igbo ke yi na a basu shugabancin kasa a 2023, Shekarau yace, “daidaito ne kawai. Ya kamata ayi da kowa.”

“Kundin tsarin mulkin Najeriya ko na jam’iyyar bai ce idan ni dan Arewa ne, wajibi ne mataimaki na ya zo daga kudu ba.” “Ba ya rubuce, amma idan yau na zama dan takaran kujeran shugaban kasa daga Kano, kuma na fada muku mataimaki na dan Bauchi ne, za kuce akwai matsala tattare da ni.”

“Arewa tayi shugabancin kasa na shekaru takwas. Aikin hankali shine mu duba dayan bangaren, Mulki ya koma kudancin Najeriya.”

Related posts

Leave a Comment