Yemen Ta Jefa Roka A Kasar Saudiyya

Hukumomin Saudiyya sun ce sun kakkabo wasu makaman roka uku da aka harbo musu daga Yemen, gamayyar sojin da Saudiyya ke jagoranta da ke yaki a Yemen ta ce daya daga cikin makaman an harba shi ne kan wata rijiyar man kasar da ke yankin gashi.

Kafafen yada labarai na cikin gidan Saudiyya na cewa yara biyu sun jikkata yayin harin wanda aka kai Kauyen Damman dake wajen gari.

Gamayyar ta kara da cewa ta lalata wani wani makamin roka da aka harba biranen Najran da Jazan da ke yankin kudancin Saudiyya.

Sun kuma ce sun tarwatsa wani jirgi maras matuki da shi ma aka harba yankin.

Har yanzu dai mayakan Houthi ba su ce komi ba kan rahoton harin.Article share tools

Related posts

Leave a Comment