Yawaitar ‘Ya’yan Gaba Da Fatiha Na Barazana A Kasar Iran – Rahoto

Rahoton BBC Hausa

“Dole ne na zubar da cikin jaririn nan. Wannan wani mataki ne mai tsauri a rayuwata,” a cewar Mitra, ?ar shekara 27 mai aikin ?awata gidaje da ke zaune a Tehran da abokin zamanta.

Mitra da Mohsen, likita mai shekaru 32, sun tare a gida ?aya ?ar?ashin wani tsarin aure – tsarin da mace da namiji za su amince su sadu da juna inda kuma yin jima’i kafin aure haramun ne ?ar?ashin dokokin musulunci na Iran.

“Mohsen da ni mun fahimci ?alubalen da ke gabanmu amma ba mu da wani tanadi na haihuwa a lokacin,” a cewarta.

Yanzu kuma sun sauya ra’ayi inda suke neman samun takardar shaidar haihuwa ga jaririn da za su haifa. Amma duk da ?o?arin da suka yi, dole ce ta tursasa masu tunanin zubar da cikin.

Ayar dokar Iran ta 1167 ta bayyana cewa “jaririn da aka haifa ta hanyar zina ba zai kasance huruminsu ba,” wanda hakan ke nufin iyayen da ba su da aure ba su da ha??in rikonsa a matsayin ma’aurata kuma mahaifiyar ce kawai za ta iya neman bu?atar a saka sunanta ita ka?ai a takardar haihuwar jaririn.

Ga jaririn kuma, hukumomi sukan adana bayanansa da yadda aka haife shi – wasu bayanai da za su hana su samun wasu ayyuka a gaba.

Duk da cewa babu adadi na hukuma kan irin wannan tsarin tarayyar, amma ya zama gama-gari.

Kuma, bayan gaza magance tsarin, hukumomi na fuskantar ?alubale na magance matsalar da kuma abin da za a yi da yaran da aka haifa ta hanyar nau’in irin wannan tarayyar.

“Daga ?arshe, wa?annan yaran dole su kar?i takardun haihuwarsu domin samun damar shiga makaranta,” kamar yadda mataimakin ministan kula da harakokin matasa Mohammad Mehdi Tondgouyan ya shaida wa kamafanin dillacin labarai na IIna.

Ya yi garga?in cewa gaza magance matsalar babban ?alubale ne.

‘Ba za mu ha?ura ba’

Ko da yake suna sane da batun makomar yaran da aka haifa a tsarin na zaman dadiro, ka?an ne daga cikin fitattun mutanen Iran suka fito suka yi magana game da batun.

Tsohuwar ?ar majalisa mai da’awar kawo sauyi Parvaneh Salahshouri ta ta?a magana a watan Satumban da ya gabata, lokacin da ta yi garga?in cewa zubar da ciki shi ne kawai za?i ga matan da suka yi ciki.

Amma Ms Salahshouri ta sha suka inda wasu suka bayyana kalamanta da “i?irarin da ba ya da tushe”.

Wasu na ganin ?alubalen tattalin arziki da kuma wasu al’adu kafin aure na ingiza ?an Iran daga tsarin da ya dace aka amince da shi na aure.

Wasu har ana karfafa wa masu tasowa gwiwa kan tsarin, ta hanyar ba su tallafin da ba ku?in ruwa.

“Wannan abin takaici ne”, in ji Shina ?ar shekara 31 daga garin Hamedan da ke yammaicn ?asar.

“Yaya batun biyan hayar gida,” a cewarta tare da bayyana damuwa kan tsadar gidaje da kuma hauhawar farashi a shekarun baya.

Shina tsawon shekaru 10 ta shafe tare da saurayinta Sadegh, kuma ta ?auki tarayyarsu a matsayin hanyar bijerewa hukumomin Iran.

“Ba mu yarda da wannan tsarin tilastawa ba na (aure),” in ji ta. Ta yaya saboda ?in amincewa da wasu sharu??a zai haramta tarayyarmu?”

Ana ganin wannan ba ?oyayyen abu ba ne tsakanin ?an Iran musamman a kafofin sada zumunta na intanet – kuma wata alama ce da ke nuna cewa tsangwama ta fara tafiya.

Manhajar Telegram ta kasance kafar da Iraniyawa ke neman masoya, ?aya daga cikin shafin yana da sama da mabiya 45,000 wa?anda suka ya?a bayanansu da nufin samun masoya.

Amma har yanzu makomar irin wa?annan mutanen na tsaka mai wuya musamman daga manyan masu tsattsauran ra’ayi masu adawa da tsarin.

‘An tarwatsa burinmu’

Ga Shina da Sadegh, matakan na yanzu suna da tasiri da tsada sosai.

Masoyan sun nemi biza a Jamus lokacin da Shina ta samu ciki a 2016, tare da sanin matsalolin shari’a da za su fuskanta da ?ansu. Amma an ki yarda da su.

“An twarwatsa burinmu kuma zubar da cikin ne kawai mafita,” kamar yadda Shina ta bayyana.

Iran ta haramta zubar da ciki har sai idan cikin na barazana ga lafiyar mace. Saboda wannan dokar, babu kwayoyin zubar da ciki a kasuwa, kuma yawancin mata ana tilasta masu amincewa da mummunan hanyar da aka haramta ta zubar da ciki da ke barazana ga lafiyarsu.

Wata ?ar shekara 36 da ta nemi a sakaya sunanta saboda dalilai na tsaro ta ce sau uku tana zubar da cikin da ta samu ta hanyar da ba ta dace ba a wata asibiti mai zaman kanta a Tehran.

Ga wasu, ficewa Iran wani za?i ne gare su.

Pari da saurayinta Yassin, wa?anda dukkaninsu ?an shekara 35 ne sun kashe dukkaninsu kudinsu domin sayen gida a Istanbul na Turkiyya, birnin da ya kasance ma?uyar Iraniyawa saboda halin ta?ar?arewar tattalin arziki da kuma rashin samun walwala.

“Lokacin da na fara fahimtar ina da ciki na yanke shawarar cewa ba zan zubar ba a wannan karon, duk kuwa da abin da zai biyo baya,” in ji Pari, wacce ta ta?a zubar da ciki.

“Barin ?asarmu ba ?aramin abu ba ne. Amma za su yi renon ?anmu cikin soyayya, kuma abin ya fi muhimmanci kenan,” a cewarta.

“Har yanzu, ba zan iya daina tunanin saduwa da abokai na ba, wa?anda ke burin samun haihuwa kuma an hana su samun damar.”

Related posts

Leave a Comment