‘Yan Bindiga Sun Yi Yunkurin Hallaka Sarkin Birnin Gwari

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga ?auke da muggan makamai sun budewa tawagar Motocin mai Martaba Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II, wuta akan hanyarshi ta komawa birnin Gwari bayan kammala taro a Kaduna.

An ruwaito cewa ‘yan Bindigar sun kai wa motocin sarkin hari ne a hanyar Kaduna zuwa Birnin-Gwari da yammacin ranar Talata, bayan kammala halartar wani taro da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, wanda ya gana da Sarakunan gargajiyan jihar ranar Talata.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa Sarkin bai cikin motar lokacin da harin ya auku. Direban Sarkin, Umar Jibril, ya bayyana cewa sarkin na wani wuri lokacin.

A hirarsa da manema labarai Umar Jibril ya ce ‘yan bindigan sun budewa motocin wuta kuma shine a gaba amma Allah ya kiyayeshi.

“Bamu tsaya ba, sun harbo min bindiga amma cikin ikon Allah harsashin bai same ni a kai ba,” yace. Ya ce sabanin kananan raunuka da suka samu, babu wanda ya jigata.

Birnin Gwari na cikin kananan hukumomin jihar Kaduna da ‘yan bindiga suka addaba.

Related posts

Leave a Comment