Rahotannin dake shigo mana daga ?aramar Hukumar ?an?ara ta Jihar Katsina na bayyana cewar wasu ‘yan Bindiga bisa Babura ?auke da muggan makamai sun kutsa wata majami’a inda suka yi awon gaba da tarin wasu mutane da ke gudanar da Ibada a a ciki.
Shugaban cocin Katolika na ?aramar hukumar ?an?ara a jihar Katsina, Ravaran Yusufa Haruna ya tabbatar da sace masu ibada tara a ?auyen Gidan Haruna.
A cewarsa, maharan sun jikkata mutum ?aya a harin da suka kai a ?arshen mako.
Ya ce “?an ta’adda sun zo suka same su suka tafi da mutum bakwai da yara guda biyu kuma sun bugi wani da sanda sun karya shi a hannu.”
Kuma duk da i?irarin hukumomi cewa suna mur?ushe ?an fashin da sauran ?an bindiga, har yanzu mazauna ?auyuka da wasu garuruwan ?asar na ci gaba da ?an?ana ku?a a hannun irin wa?annan ?atagari.
