Rahotonni da muke samu daga majalisar dokokin tarayya na bayanin cewar Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bayyana aniyar majalisar na gayyatar ministar ku?i, Zainab Ahmed, domin tazo ta musu bayani akan wasu bu?atun da ?ungiyar Likitoci ta ?asa NARD ta shigar na dalilin tsunduma yajin aiki a kwanakin baya.
A ranar Asabar ?in data gabata ?ungiyar likitoci NARD ta janye yajin aiki da ta fara tun 1 ga watan Afrilu bayan ?ulla yarjejeniya da gwamnatin tarayya.
Likitocin dai sun shiga yajin aiki ne saboda rashin cika musu al?awurra da gwamnatin tarayya tayi na ku?a?en da suke binta, da sauran wasu bukatu da suka bayyana.
A jawabin da yayi lokacin da suka yi taro da ?ungiyar ta NARD ranar Talata, Shugaban Majalisar wakilai Gbajabiamila, ya ce majalisarsu zata gayyaci ministar ku?i don su tattauna da ita kan yadda za’a kutsa bu?atun NARD a ?arin kasafin ku?i da ake yi.
Kakakin majalisar ya ?ara da cewa: “Ko kundin tsarin mulki ya yi magana a kan ayyuka masu muhimmanci, amma babu wani aiki da yafi kare lafiya muhimmanci.” “Za mu saka ido don ganin an yi abinda ya dace kan dukkan bu?atun ?ungiyar NARD.”
“Za mu yi duk abinda zamu iya kuma muke da damar yi, zamu gayyaci ministar ku?i a mako mai zuwa saboda mu tattauna yaza’a yi mu saka wa?annan bu?atun naku a ?arin kasafin ku?i.”
Kakakin majalisar ya ?ara cewa sun za?i su zo su gana da shugabannin Likitocin ne a hedkwatar su don su nuna jin da?in su kan janye yajin aikin da suka yi.
“Ziyarar da muka kawo muku na nuni da cewa muna tare da ku saboda muhimmancin likitoci bazai misaltu ba, kuma muna godiya a gareku da kuka janye yajin aiki.” “Mun zo nan ne mu gode muku bisa janye yajin aiki kuma mu ?ara baku tabbacin majalisar mu tare da majalisar zartarwa, zasu yi duk abinda ya kamata ayi.”
A jawabinsa, shugaban ?ungiyar likitocin ya nuna jin da?insa da ‘yan majalisar wakilan suka kai musu ziyara, Ya kuma gode ma majalisar kan saurin shiga maganar da ta yi wanda hakan yasa ?ungiyar ta janye yajin aikin.
