Yadda Jaruma Fadila Muhammad Ta Rasu – Mahaifinta

Rasuwa fitacciyar jaruma Fadila Muhammad a daren jiya ta girgiza masana’antar finafinai ta Kannywood matu?ar gaske.

Mujallar Fim ta gano cewar ta rasu ne a jiya Juma’a, 28 ga Agusta, 2020, da misalin ?arfe 11:00 na dare a cikin motar mahaifin ta a lokacin da ya ?auke ta zai kai ta asibiti.

Da ma ta na fama da ciwon zuciya. Tun a shekaranjiya Alhamis ciwon ya tashi, aka kai ta asibiti ta ?an samu sau?i aka dawo da ita gida a ranar. A daren jiya kuma ciwon ya yi dawowar ?arshe.

Fadila ta rasu ta na da shekara 27 a duniya.

An yi mata sallah da misalin ?arfe 8:30 na safiyar yau a nan gidan iyayen ta da ke Fagge Close, Unguwar Dosa, Kaduna, daga nan aka kai ta makwancin ta.

Marigayiyar ta kai kimanin shekara takwas a Kannywood, inda ta yi finafinai da dama.

An fi sanin ta da fitaccen fim ?in ‘Hubbi’ na kamfanin Adam A. Zango, kuma ta fito a fim ?in sa na ‘Basaja’.

Wannan mutuwa ta girgiza ‘yan fim matu?a, kowa na ta yi wa Ummi addu’a, musamman a soshiyal midiya inda da yawa su ka ri?a saka hotunan ta da kuma guntayen bidiyo daga wa?o?in ta a finafinai.

Wakilin mujallar Fim, wanda ya halarci jana’izar Ummi, ya zanta da mahaifin marigayiyar bayan an dawo daga ma?abarta game da wannan babban rashi.

Malam Muhammad ya ce, “Wannan rashi da mu ka yi babu abin da zan ce sai Allah ya ji?an ta da rahama, Allah ya sa Aljannar Firdausi ta zama makoma a gare ta” Ya na fa?in haka sai ya fara kuka.

Ya ci gaba da cewa: “Wannan yarinya babu abin da zan ce mata sai Allah ya saka mata da alheri, Allah ya yi mata sakayya da gidan Aljanna.

“Yadda wannan yarinya ke yi min biyayya, Allah na gode maka da ka amshi ran wannan yarinya a hannu na!”

Ya ci gaba da fa?a wa wakilin mu cewa: “Kai dai ganau ne, tun daga gida zuwa gidan ta na gaskiya ka ga irin ?an’adam da su ka halarci jana’izar ta.

“Kuma rasuwar yarinyar nan, in da Allah ya ?adarta sanadiyyar wani abu ne na ?acin rai, ka ga mutum ba zai damu ba; za ka ga ka haifi yaro, in ya mutu ba ka damu ba ko kuma ka ce gara a kashe shi ma. Amma ka ga ‘yan’uwa da abokan arziki da iyaye kowa na zub da hawaye. Na san dai wannan yarinya Alhamdu lillahi!

“Kuma kullum addu’ar ta Allah ya kar?i rayuwar ta kafin nawa, don ba ta son ni in rasu in bar ta.

“Abin da zan rin?a tunawa game da ita, a kullum burin ta me za ta yi min da zai sa na samu sau?in rayuwa.”

A game da maganar su ta ?arshe da Fadila, Malam Muhammad ya ce: “Jiya na ?auke ta zan kai ta asibiti, ta ce min, ‘Baba ka yi ha?uri, na ga ka na ta wahala da ni.’ Sai na ce mata, ‘Ai ba siya ki ka yi a kasuwa ba, fata na dai Allah ya sa mu yi ?arshe mai kyau daga ni har ke.’ Wannan abu ba zan ta?a mantawa da shi ba!”

A nan ma sai shau?i ya fizge shi, ya shiga kuka.

Daga baya, sai dattijon ya iske wakilin mujallar Fim a inda ya ke tsaye, ya ba shi sa?o zuwa ga ‘yan fim duka, ya ce: “Ku ke hul?a da ‘yan fim ?in nan da sauran jama’a. Don Allah ku taimake ni ku fa?a wa mutane in da wanda ke da wani al?awari na bashi tsakanin shi da Ummi, don Allah kada ya yi ?asa a gwiwa, ya zo har gida na ya sanar da ni.”

Mujallar Fim ta tuntu?i shugabar ?ungiyar masu shirya finafinan Hausa ta ?asa (MOPPAN), reshen Jihar Kaduna, Hajiya Fatima Ibrahim (Lamaj), wadda ita ce sanadiyyar shigar marigayiya Fadila harkar fim, don ‘yar kamfanin ta ce, bayan zuwan su Fati Washa kamfanin, ya tambaye ta game da wannan rashi.

Sai Lamaj ta ce, “Allahu Akbar! Babu abin da zan ce sai dai in yi wa Allah godiya domin shi ne ke raya mutum, kuma shi ke ?aukar abin sa. Ina ganin bayan iyayen ta, sai ni aka yi wa wannan rashi, don babu wanda ya ji wannan mutuwar kamar ni.

“Kwana biyun nan ba na iya bacci, sai bayan asuba na ke samun bacci, shi ya sa ban samu zuwa jana’izar ba, don ban san da rasuwar ba, ina dai jin kai na wani iri, na rasa gane abin da ke damu na, ashe labarin rasuwar Ummi zan ji!

Related posts

Leave a Comment