Ya Zama Wajibi A Yi Gaggawar Zaman Mukabala Da Abdul-Jabbar – Sheikh Yabo

Shahararren Malamin addinin Musulunci a Nigeria, Sheikh Bello Aliyu Yabo Sokoto, ya yi kira ga gwamnatin Kano, da ta gaggauta sanya zama tsakanin Malaman Kano da Zindi?i Abduljabbar.

Shehin Malamin ya bayyana cewa: “Bai yiyuwa a ta?a mutuncin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallama), sannan a shashantar da maganar, domin mun ji wani ya zagi Buhari, Gwamna Ganduje ya ?aukar masa mataki cikin gaugawa, shin kai Ganduje kana nufin mutuncin Buhari ya fi na Manzon Allah?”.

Shehin Malamin ya ci gaba da cewa: “Ba za mu daina wannan magana ba har sai an yi zaman nan”.

Shehin Malamin ya ?ara da cewa: “Duk wanda ya kar?i ku?i don lalata wannan magana Allah Ya sa su zama bala’i a gare shi.

Related posts

Leave a Comment