Gwamnan jiha Borno Babagana Zulum ya roki gwamnatin tarayyar Najeriya ta nemi taimakon sojojin kasar Chadi wurin yaki da ‘yan ta’adda domin kawo karshen zubar da jinin bayin Allah a yankin Arewa maso Gabas da ma Najeriya baki daya.
Zulum ya yi wannan jawabin ne yayin da ya tarbi wasu gwamnoni a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Laraba.
“Ina mai roko ga gwamnatin tarayya ta tabbata ta gayyaci sojojin Chadi su taimaka wa sojojin Najeriya wurin yaki da ‘yan ta’addan idan har ana son samun nasara,”.
“Babu wata rundunar soji a duniya da ta yi nasarar kawar da ta’addanci ita kadai ba tare da ha?in gwiwa ba, hakan yasa nake kira ga gwamnatin tarayya ta duba hanyoyin da za ta yi aiki da sojojin Chadin don taimakawa sojojin Najeriya don kawo karshen ta’addancin cikin kankanin lokaci.”
Ya koka ka yadda ‘yan ta’addan suka mamaye dajin Sambisa da Tafkin Chadi suka kori miliyoyin al’ummar da ke zaune a yankunan a baya.
Kayode Fayemi, shugaban kungiyar gwamnoni, NGF, wadda ya jagoranci tawagar ya ce duk abinda ya samu dayansu kamar ya sami dukkansu ne.
Fayemi ya bada gudunmuwar Naira miliyan 100 ga jihar Borno a madadin ?ungiyar gwamnoni don taimakawa al’ummar jihar.
Ya kuma bukaci gwamna Zulum ya rika takatsantsan da rayuwarsa duk da cewa sai lokacin da Allah ya kaddara mutum kwanan sa sun kare zai mutu.
