Da yake zantawa da manema labarai a birnin Ikko na Jihar Legas, Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Najeriya Amaju Pinnick ya tabbatar da cewa hukumar za ta nemi sabon kocin ‘yan kwallon kasar nan ba da dadewa ba.
Shugaban hukumar yace sun zauna da Serbian Mladen Krstajic da Jose Mourinho a yunkurinsu na neman kwararren kocin da zai rike tawagar Super Eagles na kasar.
“Mun yi magana da to Mladen (Krstajic) amma bayan nan ya samu aiki da Maccabi Tel Aviv. Haka Jose Mourinho, ba zan ce maku ba mu yi magana da shi ba.
“Ni da Ministan wasanni mun yi magana da Mourinho, kuma babu wata matsala yin hakan.”
Jose Mourinho ya na cikin masu horas da ‘yan wasan da suka fi shahara a Duniya. Mourinho ya yi aiki da Chelsea, Real Madrid, Inter Milan da Manchester United.
Rahoton Republic World yace albashin Jose Mourinho duk shekara ya kai kimanin fam miliyan €4m zuwa €7m. Sama da Naira biliyan biyu kenan a kudin Najeriya.
Shugaban Hukumar kwallon kafan ya kuma shaidawa manema labarai cewa Jose Peseiro ya na cikin wadanda suke hari. Peseiro ya taba aiki da Real Madrid, yanzu shi ne kocin FC Porto.
Shugaban yace abin da suke nema shi ne kocin da zai iya horas da ‘yan wasa da kyau. Abu na biyu a nemi wanda yake da kwadayin cin kofi da tawagar.
