?an wasan Barcelona, Lionel Messi, ya ce yana da burin wata rana ya taka leda a Amurka, amma ya ce bai da tabbacin abin da zai faru nan gaba idan kwantiraginsa ta ?are a watan Yuni.
?an ?asar Argentinar mai shekara 33, zai iya fara ciniki da kulob-kulob na ?asashen ?etare a watan Janairu.
Ce-ce-ku-ce kan makomar Messi a nan gaba ya ?aru matu?a tun bayan da Messi ?in ya nemi barin kulob ?insa a watan Agusta.
“Ban san me zan yi ba tukuna,” haka Messi ?in ya shaida wa tashar talabijin ta La Sexta ta Sifaniya.
“Zan jira sai ?arshen kaka. Ina so na taka leda a Amurka domin sanin ya rayuwa take a can da kuma sanin yadda League yake a can, amma kuma zan dawo Barcelona da sauran ?arfi na.
“A yanzu, abu mafi muhimmanci shi ne na mayar da hankali kan kulob ?ina na kammala wannan kakar da kyau, da kuma mayar da hankali wurin cin kofuna kada wani abu ya ?auke min hankali”.
Barcelona, wadda ba ta ci kofi a kakar da ta gabata ba, ita ce ta biyar a La Liga bayan sun yi wasa mafi muni a farkon gasar cikin shekara 33.
Tun bayan da Messi ya shiga Barcelona lokacin yana da shekara 13, Messi ya zama wanda ya fi zama zakara a tarihin kulob ?in ta ?angaren cin ?wallaye, inda ya ci La Liga 10, da kuma gasar Champions League sau hu?u da kuma lambar yabo ta Ballon d’Or sau shida – wadda lambar yabo ce da ake ba ?an wasan ?wallon ?afa da ya fi shahara a duniya duk shekara.
Yun?urin da ya yi a kwanakin baya na barin Barcelona ya ci karo da ra’ayin shugaban kulob ?in, Josep Maria Bartomeu, wanda ya sauka a watan Oktoba.
“Wannan wani yanayi ne mai wuya ga kulob ?in, amma wa?anda ke cikin kulob ?in sun san yana cikin mawuyacin hali, abubuwa sun lalace kuma yana da wahala kulob ?in ya koma yadda yake a baya,” a cewarsa.
