Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar uwargidan shugaban ?asa Aisha Muhammadu Buhari, ta umarci ma’aikatan ofishinta su fara hutun sai baba ta gani, a wani ?angare na tunkarowar ?arshen shekara da kuma bikin kirsimeti.
Cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafinta na Instagram, an bayyana cewa za a rufe ofishin ?ungurngum, har abun da hali ya yi.
”Za a iya ri?a gudanar da muhimman ayyuka ta Internet kamar yadda aka yi a baya’, don haka daga yanzu kowa ya tafi hutu sai an ji daga garemu’ kamar yadda aka sanar da ma’aikatan cikin wannan sanarwa da ke ?asa.
