Uwargidan Gwamnan Kaduna Ta Sanya Gasa Kan Ya?i Da Matsalar Fya?e

A daidai lokacin da aka cika kwanaki 16 da fara gwagwarmayar ya?i da matsalar fya?e da cin zarafin ?a?a mata da yara ?anana wacce aka fara (daga ranar 25 ga watan Nobemba zuwa 10 ga watan Disamba, 2020) uwar gidan gwamnan Jihar Kaduna, Ummi Garba El’Ru’i, ta ha?a gasa mai taken: #ummielrufaisgbvchallenge!

“Akwai bu?atar gaba ?ayanmu tare da jarumai mu mara baya akan ya?i da matsalar cin zarafin jinsi saboda yaranmu ?anana maza da mata da ?an mata da mutane masu bu?ata ta musamman, gaba ?aya su na bu?atar kariya”. Inji Aisha-Ummi El-Rufai

Gasar ?alubalen wacce ta jawo hankali matu?a a sabbin kafafen sadarwa na zamani, ta bu?aci al’umma su bazu a wuraren da su ke rayuwa su dauki bidiyo na mintuna 2:30 suna wayar da kan jama’a kan abunda ya kamata su sani kuma su yi a lokacin da aka samu hatsarin fya?e, su yi bayani akan hatsarin da kuma bada hanyoyin kariya kan fafutukar ya?i da matsalar wajen bincike da hannata lamarin ga rundunar tsaro.

A ?arshen gasar ?alubalen mai taken: #ummielrufaisgbvchallenge?, uwar gidan gwamnan ta bayar da kyautar ku?ade ga wa?anda su ka lashe gasar kamar haka:-

Wanda ya zamo na ?aya su ne: @team_nonstop (a Instagram) tawagar da ta ha?a da:
@musab_jibril
@maamah.hussein
@siryunus_ibrahim
Sun samu kyautar Naira Dubu Dari Biyar da Hamsin (N550,000)!.

Wadda ta zo na biyu ita ce Amina Zakari @ummeeytarh (a Instagram) inda ta samu kyautar Naira Dubu Dari Uku da Hamsin (N350,000)!.

Sai wa?anda su ka zo na uku, su ne Marie White da Reuben Victoria inda kowanensu su ya samu kyautar Naira Dubu Dari Biyu da Hamsin (N250,000). Marie White (a Facebook), Vicky_ru (a Instgram).

“Mu na matu?ar alfahari da ku, mu na fatan ?wazonku zai cigaba da taimakawa wajen wayar da kan jama’a game da ya?i da matsalar fya?e da sauran nau’ikan cin zarafi”. Inji Aisha-Ummi Garba El-Rufa’i, matar gwamnan jihar Kaduna.

Ummi ta kuma yabawa ?wazon duk wa?anda su ka fafata a gasar ta neman jawo hankalin jama’a a mara baya kan ya?i da matsalar fya?e da sauran dangogin cin zarafin mutane musamman mata da ?ananan yara.

Baya da haka, ta kuma ?ara da baiwa wasu daga cikin wa?anda su ka taka rawa kyautar lambar yabo ta ku?i domin ?arfafa musu gwiwa. Kowane mutum ?aya ta bashi Naira Dubu Dari-Dari (N100,000). Mutanen da ta ba wa sun ha?a da:

  • BeeJayzphotos (Facebook)
  • Aysha Ahmad ~ elgashash
    Musa Sa’ad (Instagram)
  • Shamzik Care Foundation (Instagram)
  • Blessing Okebugwu (Instagram)
    @blessingOkebug2 (Twitter)

*Bello idris (Instagram)
@belloyombi (Twitter).

Sai kuma wadda ta taka rawa na musamman Pamelagold Ojoma Hassan; wacce bidiyon da ta samar ya fi na kowa ta samu Naira (N200,000)! o.j.o.m.a_ (Instagram).

“Mu na matu?ar alfahari da ku, sannan mu na fatan za ku kasance abokan hul?armu wajen ya?a ?umbin sa?onni a nan gaba”. Inji ta.

Daga ?arshe ta kuma yi godiya da yabawa da ?wazon kwamitin al?alan gasar da ta kafa wa?anda ta jagoranta:
UNFPA (@unfpakd)

Mariama Darboe, jagorara shirye-shirye ta UNFPA na Kaduna Kaduna – (@mariamaDarboe18)

Hafsat Kagara, mai ba da shawara ta fannin shari’a a UNFPA kan ya?i da mtsalar fya?e da cin zarafi a Jihar Kaduna (@kagara_hafsy).

Professor Hauwa Evelyn Yusuf, Farfesa akan ilimin jinsi da binciken gano masu laifi (Criminology and Gender Studies, KASU – (@ProfHEY1).

Madam Juliana Joseph – (@SalamaSarc) manajar cibiyar. Salama SARC.

Adejoke Fayemi, shugaban sashe (Head of Station, Raypower – (@favouredjoke)

Dakta Binta Kasim Mohammed, Associate Professor of Mass Communication, KASU – (@Bazazzaga)

Dakta Zubaida Abubakar, Gender/GBV Specialist UNFPA Nigeria – (@ab_zubaida).

Related posts

Leave a Comment