Uwargidan Ganduje Za Ta Tsaya Takarar Sanata

Mai ?akin gwamnan jihar Kano Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta fara shirye-shiryen neman kujerar ?an majalisar dattawa a shiyyar Jigawa ta Yamma maso Gabas a za?en shekarar 2023 da ke tafe.

Wata majiya mai ?arfi da ta ke kusa da Dakta Hafsat Ganduje wacce ?ar asalin ?aramar hukumar Malam Madori ce da ke jihar ta Jigawa, da ta bu?aci mu sakaye sunanta ta bayyanawa Labarai24 cewa tabbas akwai shirin yin takarar na Hafsat Ganduje ?in.

Majiyar ta ?ara da cewa tuni shirye-shirye sun yi nisa domin har ta fara tuntu?ar masu ruwa da tsaki tare da kungiyoyin matasa da ke maza?ar ta Jigawa maso gabashin jihar.

“Maganar gaskiya akwai maganar takarar da Gwaggo ta ke shirin yi a jihar Jigawa, amma kawo yanzu ba ta fito ta sanar ba”

“Domin ko a lokacin da ake sabunta katin rijistar jam’iyyar APC, to ba na Kano ta yi ba, kuma ba ta bayyana cewa ta tafi Jigawa ta yi ba. Har gida aka zo aka yi mata daga jihar ta Jigawa”

Lokacin da aka sabuntawa Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje katin jam’iyyar APC

Aikin samar da rijiyoyin burtsatse a mazabun karamar hukumar Malam Madori da Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta yi. Haka kuma wakilin Labarai24 ya je har ?aramar hukumar Malam Madori inda nan ne mahaifar Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje din inda ya samu zarafin tattaunawa da wasu daga cikin al’ummar wannan karamar hukuma.

“Littattafai masu ?auke da hoton Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje da aka raba a wasu makarantun jihar Jigawa”

Alhaji ?ankano Mai Yadi ?aya ne daga cikin dattawan ?aramar hukumar Malam Madori ya bayyana cewa duk abin da Hafsat Gandujen za ta nema suna goyon bayanta ?ari bisa ?ari.

“Duk abin da mai girma Gwaggo za ta nema ko ma meye muna goyon bayanta ?ari bisa ?ari, saboda irin yadda ta ke taimakon al’ummar mahaifarsa”

Shi ma wani matashi mai suna Hashim Malam Madori cewa ya yi a shirye su ke wajen baiwa Gwaggon gudummawa a dukkanin wata kujera da za ta nema.

“Game da ra’ayina akan tsayawar Gwaggo takarar ina goyon baya ?ari bisa ?ari, domin matar nan ta nuna mana halacci kuma ta nuna mana ita cikakkiyar ?ar Malam Madori ce mai kishin Malam Madori, saboda haka ina ra’ayi kuma na goyi baya”

Haka kuma Dakta Hafsat Ganduje ta samar da rijiyoyin burtsatse a mazabun da ke ?aramar hukumar Malam Madori tare kuma da raba littafai ga makarantun yankin, wanda al’ummar wannan yankin ke kallon hakan a matsayin sharar fage ne na yin takarar.

Hafsat Abdullahi Umar Ganduje wacce Malama ce a jami’ar Bayero kuma tana da tasiri a cikin harkokin gwamnatin Kano za ta fafata da Barista Ibrahim Hassan Hadejia, wanda ya ta?a ri?e mu?amin mataimakin gwannan jihar ta Jigawa kuma shi ne ke wakiltar maza?ar Jigawa ta Yamma maso Gabas a zauren majalisar dattawan ?asar nan.

Haka kuma ?ananan hukumomi guda takwas ne ke karkashin wannan maza?a. ?ananan hukumomin da su ka ha?a da Auyo da Birniwa da Guri da Hadejia da kuma Kafin Hausa.

Sauran ?ananan hukumomin sune Kaugama da Kirika Samma da sauransu.

–Labarai24

Related posts

Leave a Comment