Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Gwamnatin ta nemi iyayen ?alibai a ?asar da su ro?i malaman jami’a su jingine yajin aikin da suke yi tsawon wata biyar “saboda ta yi abin da za ta iya”.
?aramin Ministan ?wadago Festus Keyamo ne ya bayyana hakan yayin da ya bayyana ta cikin shirin Politics Today na kafar talabijin ta Channels a yammacin Juma’a.
Ministan ya ce tun kafin ?ungiyar malaman ta ASUU ta fara yajin aikin gwamnati ta kira su don tattaunawa amma duk da haka sai da suka tafi yajin aikin.
Da aka tambaye shi ko me zai fa?a wa iyayen da yaransu ke ci gaba da zaman gida har yanzu, sai ya ce: “Zan ce musu su je su ro?e su [ASUU]. Kamar yadda shugaban ?asa ya fa?a a baya, wa?anda suka san su su ro?e su don nuna kishinsu ga ?asar.”
Ya ci gaba da cewa: “…Me za mu yi fiye da haka? Tun kafin a fara yajin aikin muka kira su. Ba wai ?yale su muka yi ba kawai muka kama barci. Ba zai yiwu ka ?yale mutum ya ci kwalarka ba kuma ya tilasta maka ciyo bashin naira tiriliyan ?aya.”
A farkon makon nan ne ASUU ta sake tsawaita yajin aikin da take yi da mako hu?u, ?ari a kan wata biyar da ta shafe bayan jingine aiki a jami’o’in Najeriya.
