Tsoron ‘Yan Bindiga Ya Sa Na Cire ‘Da Na Daga Makarantar Gwamnati – El Rufa’i

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufa’i yace ya cire ?anshi ne daga Makarantar Gwamnati, saboda tsoron ka da ‘yan Bindiga su sace shi sakamakon lalacewar tsaro.

Gwamnan ya bayyana cewar tun da fari ya sanya ?anshi a Makarantar Gwamnati domin tabbatar da ?udirin sa na yarda da tsarin ilmin Jihar Kaduna.

El-Rufa’i ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokacin jawabin da ya gabatar a Kwamitin Shugaban ?asa kan Sadarwa a birnin tarayya Abuja.

Ya bayyana cewar, Gwamnati ta ?auki Malamai da yawa, fiye da wanda ta kora daga aiki a shekaru biyar, yana mai ?ara da cewa an ?auki ?wararrun Malaman Sakandire guda dubu 7,700, kuma za su fara aiki da zaran mun cire bara gurbi daga cikin su.

“Mun kori Malamai dubu 22,000 mun ?auki mutane dubu 25,000. Munyi masu Jarabawa,wasu sun ?ara fa?awa sun kuma fa?i. Zamu kore su, mu dauki wasu. Mu a shirye muke mu inganta ?wazon Malamai, domin malami shine ilmi, ba aji ba.

“Duk muna tunanin cewa ?ata garin suka je Makarantun Firamare. To yanzu dole ne zamu jijjiga Malaman Sakandire suma. Mun ?auki Malamai dubu 7,700. Mun ?auki matsaya cewa zamu tura ?iyan mu a Makarantun Gwamnati.

“Na kai yaro na Makarantun Gwamnati, domin mu nunawa Al’umma cewa mun aminta da tsarin ilmin Makarantun Gwamnati, amma dole in cire shi, saboda ?o?arin sace shi kuma bana tunanin zasu yi nasara, amma zasu sanya yaran mutane a cikin hatsari.

“Na cire shi ne. Yanzu yana kar?ar ilmi a gida har sai munga yanda yanayin ya bada,” inji Gwamnan

Related posts

Leave a Comment