Allah Ya yi wa tsohon shugaban rikon kwarya na Najeriya Cif Ernest Shonekan rasuwa kamar yadda rahotanni da dama a kasar suka tabbatar..
Cif Shonekan ya mutu ne a wani asibiti a birnin Legas ranar Talata, kamar yadda rahotannin suka nuna.
Tsohon shugaban rikon kwaryar ya mutu ne yana da shekara 85 a duniya.
Cif Shonekan ne shugaban gwamnatin rikon ?waryar Najeriya daga tsakanin 26 ga watabn Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamban 1993.
Marigayi Janar Sani Abacha wanda shi ne Sakataren Tsaro na kasar a lokacin, ya hambarar da gwamnatin ri?o ta Cif Shonekan cikin ruwan sanyi ba tare da zubar da jini ba a Nuwamban 1993.
Shonekan ya mi?a mulki ga sojoji bisa dole da kuma umartarsa ya rattaba amincewar sauka daga kan mulki; inda ya yi hakan kan takarda da aka rawaito cewa babu ko tambari ko hatimin gwamnatin Najeriya a takardar.
Mutuwar Cif Earnest Shonekan ta zowa da mutane da yawa da ba zata duk da cewa shekarunsa sun ja; to amma bisa la’akari da ?warewarsa kan harkokin kasuwanci da kuma kar?uwa ta kamala cikin al’umma ya sanya ake cike da alhinin mutuwarsa.
Tuni ?an Najeriya suka fara alhinin mutuwar tasa kuma da dama sun ce za su dinga tunawa da marigayin a matsayin shugaba na gari, yana da buri mai kyau ga Najeriya, duk da cewa bai da?e akan mulki ba aka tun?uke shi.
Wasu kuma na cewa za su tuna da Earnest Shonekan a matsayin dan kasa na gari, kuma tsohon Shugaban gwamnatin rikon kwarya a Najeriya, “yana da kyakkyawar aniyar gina ?asar, sai dai ya shiga gwamnatin kasar ta haramtacciyar hanya da ta saba da tsarin dimokuradiyya,” a cewar wani da BBC ta zanta da shi.
Ya ?ara da cewa “To amma duk da haka mun gode Allah ya kasance wani da ya ?inke ?arakar da ta so wargaza Najeriya. Ina iya tunawa cewa ya shugabanci kamfanoni masu yawa a Najeriya.”
