Tsaro Ya Inganta A Mulkin Buhari Fiye Da Gwamnatocin Baya – Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban kasa ta fito fili ta bayyana gagarumin bambancin dake tsakanin gwamnatin Shugaban Kasa Buhari da gwamnatocin baya na PDP wa?anda suka lashe shekaru 16 suna azabtar da jama’a, babu shakka tsaro da kwanciyar hankali ya samu a gwamnatin Buhari ta APC, ta yi kira ga mutanen Najeriya su godewa Allah da aka daina samun tashin bama-bamai kamar yadda aka saba yi a baya.

Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Femi Adesina, ya yi wannan martani game da kukan dadi da ‘yan Najeriya su ke yi game da sha’anin tsaro a yanzu, inda ya bayyana wannan kukan da?in zai kasance imma dai na son zuciya ko kuma na wata muguwar mantuwa da ‘yan Najeriya suka tsinci kansu a ciki.

Mista Femi Adesina ya bayyana hakan ne a shirin siyasa na Sunday Politics a gidan talabijin na Channels, a tattaunawar da aka yi da shi kai tsaye a karshen makon daya gabata.

Adesina yace kafin zuwan mai gidansa shugaba Muhammadu Buhari kan mulki, akwai lokacin da sai bama-bamai har shida su tashi a rana guda, babu wani Mutum guda a Najeriya wanda yake cikin kwanciyar hankali a wancan lokacin, an wayi gari har magidanta na rubuta wasiyya ga Iyalansu idan zasu fita saboda rashin tabbas na ko zasu dawo a raye.

A cewar Hadimin Shugaban kasar yanzu bam ba su tashi a Najeriya domin ana shafe tsawon watanni ko shekara ba tare da an samu aukuwar wannan mummunan lamari ba, jama’a ma har sun manta da cewar ana samun faruwar fashe fashen Bama bamai a Najeriya.

“Mu gode da wannan saukin da aka samu, sannan mu yaba namijin ?o?arin Shugaban Kasa Buhari akan zaman lafiya da ya ?ora Najeriya, mu kasance masu godiya sai Allah ya ?ara taimakon mu kada mu kasance masu ya?a sharri fiye da alkhairi”.

Related posts

Leave a Comment