Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Janar Babagana Monguno ya ja kunnen Gwamnan Nasiru El-Rufai game da kalaman da ya ce gwamnan na yi kan harkokin tsaro.
Monguno ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa a karshen ganawa da shugaban kasa ya yi da hafsoshin tsaro a Abuja.
“Gwamna Nasir El-Rufai ya yi magana kan hukumomin tsaron kasar nan yana cewa wai mun san ko su wane ne ‘yan ta’addan nan, da inda suke,” a cewarsa.
Monguno ya kara da cewa “wannan shi ne babban ha?arin, musamman idan ka fara maganar da ba ta dace ba, sai kai ta fadin abin da ba shi kenan ba”.
