Gwamnan jihar kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya kammala aikin sanya kyamarorin sa ido a wasu manyan titunan Kano domin ingantawa da saukaka Ayyukan tsaro A jahar Kano.
Salihu Tanko Yakasai, mashawarci na musamman kan harkokin yada labarai ne ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook, inda ya nuna bidiyon jami’an ‘yan sanda da ke kallon motsin mutane da ababen hawa a kan manyan titunan jahar kano
Duk da cewa Kano ta kasance daya daga cikin jihohin da suke da zaman lafiya a Najeriya tun shekaru biyar da suka gabata, amma Mai Girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai daina kokarin karfafa tsaro a jihar ta Kano ba
Domin kuwa gwamnatinsa ta sanya kyamarorin sa ido a kan manyan hanyoyi.
Ana aiki da na’urorin (CCTV) daga wani daki na musamman a hedikwatar ‘yan sanda, na jihar Kano. “in ji Salihu Tanko Yakasai.
