A sakon da ya fitar na murnar bikin sallah karama, Shugaban ?ungiyar IMN (Shi’a) ta ?asa Sheikh Ibrahim Yakubu El Zakzaky ya bayyana yadda ma?iya suka taso yankin Arewa gaba.
Shugaban kungiyar ta ‘yan Shi’a ya zayyano wasu abubuwa guda uku wa?anda sune jigajigan karfin arzikin Arewa kuma ake burin ruguza su.
1-Noma. wadda ita ce tushen arzikin mutanen yankin, yanzu ta gagara, an hana manoma aiki an kore su daga garuruwan su, wanda ya zauna za a kashe shi.
2-Kiwo. Makiyaya an kashe ana kwashe dabbobin su.
3-Kasuwanci. Sufurin kayayyaki ya zama hadari, saboda ayyukan ‘yan ta’adda a hanyoyi. Sai gobara a kasuwanni wadda ba ta lafiya bace a rasa mai ya haddasa ta. Dan kasuwa idan yabi hanya a sace shi a nemi kudin fansa, sai dai a kwashe jarin sa a fanso shi ya dawo ba abin juyawa.
Su kuma manyan yankin ba wannan ne ya dame su ba, in dai za a ba mutum mukami shi kenan kawai.
