Tsadar Rayuwa: Kungiyar Kwadago Ta Nemi Karancin Albashi Na 794,000

IMG 20240308 WA0067

Kungiyar Kwadago ta Bu?aci Naira Dubu 794,000 a Matsayin mafi ?arancin albashi Ga ma’aikata a yankin Kudu Maso Yamma

Kungiyar Kwadago a yankin Kudu maso Yamma ta bakin shugabar kungiyar ta NLC reshen jihar Legas, Funmi Sessi ta gabatar da bukatar a yayin gabatar da jawabinta a taron jin ra’ayin jama’a na kwamitin uku na kasa kan mafi karancin albashi a Ikeja, Legas A Yau Alhamis.

Sessi ya bayyana cewa an amince da bukatar tare da dukkanin mambobin kungiyar a yankin Kudu maso Yamma .

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ta bakin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya kaddamar da kwamitin mutane 37 kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata a zauren majalisar dokokin jihar dake Abuja a ranar 30 ga watan Janairu, 2024.

Related posts

Leave a Comment