Majalisar zartarwar Nijeriya ?ar?shin jagorancin shugaba Muhamamdu Buhari ta amince da sakin sama da naira bilyan 44 domin bada kwangilar samar da tituna a Abuja.
Aikin wanda zai gudana ?ar?shin ma’aikatar kula da babban birnin da kuma ma’aikatar ayyuka da gidaje ya ?unshi inganta samar da ruwan sha, da kuma samar da tituna a sassan ?waryar birnin.
Jaridar The Nations ta ambato ministan watsa labaran Nijeriya Lai Muhammad na cewa an amince da sakin Naira Biliyan 31,630,221,349 a kan wa?annan ayyuka.
Shi ma ministan ayyuka da gidaje Babatunda Fashola, ya ce ma’aikatarsa ta ha?a hannu da hukumar kula da ingancin tituna ta FERMA, domin tabbatar da anyi aikin yadda ya kamata.
