Shugaban ?asa Bola Tinubu, ya bukaci majalisar dattawa da ta yi wa dokar kasafi ta 2024 da kuma dokar kudi ta 2023 gyaran fuska ta hanyar amincewa da ?arin naira tiriliyan 6.2 a cikin kasafin ku?in.
Bu?atar ta Tinubu na ?unshe ne a cikin wata wasi?a da ya aika wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kuma aka karanta a zauren majalisa ranar Laraba.
A cikin wasikar, Shugaban ya ce yana son ?aukar matakin ne bisa dogaro da sashe na 58, ?aramin sashe na biyu na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa gyaran fuska.
Wasi?ar ta ce “Ana bu?atar yin gyara ga ?udirin kasafin ku?in shekarar 2024 don samar da ?arin naira tiriliyan 3.2 don ayyukan more rayuwa da sauran muhimman ayyuka da za a gudanar a fa?in ?asar.
“Da kuma naira tiriliyan uku don biyan wasu bu?atu na yau da kullum, wa?anda suka dace don gudanar da ayyukan na tafiyar da harkokin gwamnatin tarayya, wa?anda za a samu ta hanyar ku?a?en shigar da gwamnatin tarayyar Najeriya ke sa ran samu,”
Tinubu ya ?ara da cewa ana bu?atar aiwatar da gyare-gyaren da ake neman yi wa dokar ku?i ta 2023, domin a sanya haraji kan ribar da bankuna suka samu a cikin bayanan kudi na shekarar 2023.
Ya yi bayanin cewa an yi hakan ne don samar da ku?a?en da za a yi amfani da su wurin bun?asa manyan ababen more rayuwa a fannin ilimi da kiwon lafiya, da sauran ayyukan jin dadin jama’a.
