Jigo a jam’iyyar PDP, Dele Momodu, ya dora alhakin duk matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta a kan yunkurin da jam’iyyar APC mai mulki ta yi na kawo cikas ga ‘yan adawa a kasar.
Momodu, ya bayyana haka ne lokacin da ya ke jawabi a a shirin ‘siyasa a yau’ na gidan talabijin din Channels a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya zargi jam’iyya mai mulki karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da yunkurin murkushe ‘yan adawa.
APC za ta yi duk mai yiwuwa don ruguza ‘yan adawa; su sayi wadanda za su iya saya, su tsoratar da wadanda ba za su iya saya ba tare da tabbatar da cewa jam’iyyar ta wargaje.” – A cewar Momodu.
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kasa shawo kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar tun bayan faduwa zaben shugaban kasa a shekarar 2023.
Nyesom Wike, ministan Abuja ya kara dagula lamuran jam’iyyar yayin da ya karbi mukami a gwamnatin Tinubu bayan da aka yi zargin ya yaudari a zaben na 2023.
Da yake karin haske a ranar Alhamis, Momodu ya zargi Tinubu da murkushe ‘yan adawa duk da cewa shi ma dan adawa ne kafin jam’iyyarsa ta kawar da PDP daga mulki. Momodu ya kara da cewa Gwamna Similanayi Fubara da wanda ya gada, Nyesom Wike na fada ne kan yadda ake tafiyar da baitul malin jihar, inji rahoton Daily Trust. “Tinubu na amfani da Wike a Ribas. Suna son ya samu iko da jihar ba wai kawai domin nema masu kuri’u ba, har ma da ba su damar shiga baitul malin jihar Ribas.” – In ji Momodu.
