Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana sa ran tattalin arzikin Najeriya ya bun?asa da kashi uku cikin 100 a shekarar 2023.
A wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar kan yanayin bun?asar tattalin arzikin duniya a shekarar 2023, ta ce ?aruwar hauhawar farashi da ?arancin wutar lantarki na yin tasiri a kan ha?akar tattalin arzikin Najeriya.
”To sai dai tattalin arzikin zai bun?asa ta hanyar ha?akar kasuwanci da sauran sana’o’i, lamarin da zai sa bun?asar ta kai kashi uku cikin 100.”, in ji rahoton.
Rahoton ya ?ara da cewa ana sa ran samun ha?akar tattalin arziki ne a gabashi da yammacin Afirka.
Haka kuma rahoton ya yi hasashen cewar ?aruwar farashin kayayyaki zai taimaka wa masu safarar kayayyakin, to sai dai kuma ta yi garga?in cewar ruguwar ?ukatar kayayyakin a duniya ka iya haifar da kalubale.
