Taron Zaman Lafiya: A Tsaye Muke Har Sai Mun Kawar Da ‘Yan Ta’adda A Najeriya – Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce Gwamnatin sa ba za ta huta ba har sai an kawar da ta’addancin ‘yan fashi da sauran matsalolin tsaro a kasar nan.

Hakan kamar yadda ya ce kasar na fuskantar sauyi yayi a sabili da sabbin dabarun ya?i da jami’an tsaro suka ?auka ya fara bayar da sakamakon da ake bu?ata.

Shugaban ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake bayanin bu?e taron zaman lafiya da tsaro na yankin Arewa maso Yamma mai taken “Hadin kai na yankin Arewa maso Yammacin Najeriya” wanda kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma tare da hadin gwiwar hukumar ci gaban Majalisar Dinkin Duniya UNDP suka shirya a Jihar Katsina.

Tinubu wanda Mataimakin Shugaban ?asa Kashim Shettima ya wakilta a wajen taron ya ce “Abin da muke gani matsala a fadin Arewa shi ne dur?ushewar ala?a tsakanin Jihohin. Dangane da matsalar tsaro kuma dole ne mu taka musu birki, matakin da muka dauka a yanzu shi ne umartar Jami’an mu na yankin Arewa maso Yamma, da kuma Arewa maso Gabas da su tabbatar da zaman lafiya a wa?annan yankunan.

Shettima ya ce duniya na kallon Arewacin Najeriya a matsayin al’umma guda daya, yana mai cewa hadin kan yankin ya kafu ne cikin al’adu da kuma ?imanta bu?atun juna.

Related posts

Leave a Comment