Rahotannin dake shigo mana yanzu daga Jalingo babban birnin jihar Taraba na bayyana cewa, gamayyar Yan- takaran kujerun Majalisar Jiha, na Wakilai da na Tarayya da Dattawa sun tabbatar da ba a yi zaben fidda gwani a Jam’iyyar ba.
Inda rudani da rigingimu suka hana Jam’iyyar APC gudanar da zaben fidda gwani a Jihar ta Taraba
A wani yunkurin tabbatar da ganin an yi musu adalci, a taron manema Labarai da suka yi, mai magana da yawun gamayyar hadakan yan takaran Majalisar Jihar a karkashin Jam’iyyar ta APC, Barista Shitu Muhammed yace babu inda zaben fidda gwani ya gudana a duk fadin Jihar Taraba.
“Muna tabbatar wa da Duniya su sani cewa babu inda zabe ya gudana a Jihar Taraba, hasalima, ko tozali mu ‘yan takara bamu yi da wadannan Kwamitoci biyu da Uwar Jam’iyya ta turo ba, Kwamitin gudanar da zabe da Kwamitin sauraron koke-koken bayan zabe, ballantana mu zauna dasu mu fahimci juna ta yadda zaben zai wakana cikin adalci, amma kwatsam sai mukaji sakamakon zaben ya bayyana a kafafen sadarwa na zamani, wato ‘Social Media”.
Shitu ya kara da cewa ba za su lamunci duk wani tsari na rashin adalci ba, kuma ya zama wajibi Sakatariyar Jam’iyyar APC ta gaggauta daukan mataki a kan lamarin, kafin wankin hula ya kai ta dare’. “Tsarin malkin Najeriya da Dokokin Jam’iyyar APC ba a bin wasa bane, kuma ya zama wajibi a yi biyayya da shi, idan kuma ba haka ba babu abin da zai hana durkushewar Jam’iyyar APC a Taraba.
Barrista Shitu Muhammed, ya kara ankarar da uwar Jam’iyyar APC da suyi la’akari da cewa Sashi 84 (sakin layi na 1), yayi bayani karara kan yadda ya kamata wurin anfani da tsarin nan na ‘Kato bayan Kato’ a yayin zaben fidda gwani.
