Labarin dake shigo mana daga Jalingo babban birnin Jihar Taraba na bayyana cewar mai bayar da shawara ta musamman ga Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba Sale Ahmadu a ranar Alhamis, ya yi murabus inda ya ce gwamnatin jihar ta rasa alkibla.
Murabus din Ahmaadu ya zo ne kasa da wata daya bayan wani mataimaki na musamman ga gwamnan mai suna usman Sa’adu da wasu mutum biyu suka yi murabus a gwamnatin jihar.
An aike wasikar murabus din ga gwamnan ta ofishin sakataren gwamnatin jihar, Anthony Jellason inda aka ce “shekaru biyu da suka gabata sun kasance masu matukar kalubale ga rayuwa ta da imani na.
“An biya ni albashi ba tare da wani aiki ba, wanda hakan ya ci karo da addini na ballantana a gwamnati da jam’iyyar da ta rasa alkibla.
“Mulkin jihar nan karkashin shugabancin Gwamna Ishaku tafe yake ba tare da wani cigaba ba. “A don haka, ina so in shiga cikin wadanda suka saurari umarnin Ubangiji kuma suka cigaba da rayuwarsu.”
A yayin martani ga murabus din, sakataren hulda da jama’a na Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Honarabul Andeta’rang Irammae, ya musanta ikirarin cewa gwamnatin Ishaku ta rasa alkibla.
