Kwamitin tantance ‘yan takara na jam’iyyar APC mai kula da za?ukan fidda gwani na kananan hukumomin Jihar Kaduna ya fitar da sunayen ‘yan takara wa?anda suka yi nasara da wadanda basu samu nasara ba a za?en da zai gudana a ranar 5 ga watan Mayun shekara ta 2021.
?aya daga cikin ‘yan takarar shugabancin ?aramar Hukumar Kaduna ta Kudu Honorabul MS Ustaz Mesittin na ?aya daga cikin wa?anda suka samu zana jarrabawar gwaji da jam’iyyar ta shirya kuma ya yi nasarar samun maki 53.38. Wanda hakan ke nuna cewar ?an takarar ya tsallake, amma abin mamaki sai gashi bayan fitar da sunayen an cire sunan MS Ustaz cikin wadanda suka yi nasara.
Wani abin mamaki shine sai gashi wasu ‘yan takara guda biyu Rabi’u Aliyu da Sabo Aminu Anchau daga ?aramar Hukumar Kubau an bayyana su matsayin wa?anda suka yi nasara da maki 50 da 53 kowanne ?aya daga ciki. Wannan wani al’amari ne mai muhimmanci da ya kamata jam’iyya ta yi la’akari dashi.
Yana da matu?ar muhimmanci babbar jam’iyya kamar APC tayi dukkanin mai yiwuwa wajen samun ha?in kan ‘ya’yan jam’iyya ba raba kawunan su ba, domin tabbas wannan rashin adalci da aka yi zai haifar da gagarumar matsala a jam’iyyar.
Abin da ake fata shine jam’iyyar ta kare muradun ‘ya’yanta ta hanyar adalci ba biye wa son zuciyar wasu shafaffu da mai a cikin jam’iyyar ba, duk wanda ya yi nasarar a jarrabawar da aka yi a bashi damar yin takara.
Bisa ga wannan ne muke kira ga mai girma Gwamnan Jihar Kaduna, da Jam’iyyar APC ta Jihar da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, da su shigo cikin lamarin su tabbatar anyi adalci ta hanyar ba da dama ga dukkanin wa?anda suka cancanci yin takara a basu damar tsayawa takara domin kai wa ga nasarar jam’iyyar.
Daga Kwamitin ya?in neman za?e na MS Ustaz dan takarar Shugabancin ?aramar Hukumar Kaduna ta Kudu
