Wata mata mai suna Etiennette Ajoluje, ta bayyana abubuwan da ta gano da tayi cudanya da wasu karuwai a wata anguwa da ke jihar Legas, a yayin wata ziyara ta musamman da ta kai musu.
Bayan ta kai wa gidan karuwan ziyara a ranar Juma’a, 6 ga watan nuwamba, ta gano cewa karuwa guda daya tana iya samun a kalla N5000 kullum idan ta kwanta da maza 5 zuwa 7.
Ta gano kusan karuwai 4 da ke dauke da juna biyu, sai wata wacce take goyon jariri mai watanni 16 da haihuwa.
Kamar yadda Ajoluje ta bayyana, karuwan da ta tattauna da, sun tabbatar mata da cewa talauci ya jefa su sana’ar kuma a shirye suke su bar karuwanci.
Kamar yadda ta wallafa: “Suna samun N5000 idan sun kwanta da a kalla maza 5 zuwa 7 a rana.
“Watanni 3 da suka gabata, wata kyakkyawar yarinya ta same ni da hawaye share-share, tana rokona in taimaka mata ta bar rayuwar bariki.
“Karuwa ce, ta kirani kwanaki 4 da suka wuce, shiyasa nayi wannan wallafar. Na kai ta wani wurin cin abinci (Mama put) inda muka ci, muka sha. Sai da na tabbatar hankalinta ya kwanta, tukunna na tambayeta matsalarta.
“Muna samun N5,000 daga kwanciya da maza 5 zuwa 7, “Tana kwanciya da a kalla maza 5 zuwa 7 a rana, kowannensu yana bata N500 zuwa N1000.
Ta kaini gidan karuwan da take biyan N1000 kullum a matsayin ku?in ?aki.”
Na hadu da wata mata mai jariri dan shekara daya da watanni 4 da haihuwa a wannan gidan karuwan. Goma daga cikinsu cikin hawaye sun tabbatar min cewa suna so su tuba.
Akwai masu gyaran gashi, teloli, masu girke-girke da sauransu a cikinsu. Ku taimaka jama’a. Ku bani shawara a kan wannan al’amarin. Ni ‘yar sako ce.
