Ta’addanci: ‘Yan Bindiga Sun Ci Taliyar Karshe – Buhari

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya yi alla-wadai da harin da aka kai ranar Alhamis a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, yana mai cewa hari ne da aka kai wa Najeriya baki-?aya.

Shugaban da ke shaida hakan a wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu, ya fitar na cewa dole a hukunta maharan domin ba za a ta?a yafe musu ba.

Ya kuma ce harin ba zai yi tasiri a yakin da suke yi da matsalolin tsaro ba, yayinda ?asar ta hada kai domin ya?ar ‘yan tadda da miyagun mutane da ya bayyana da annoba.

Shugaba Buhari ya aike sakon ta’azziya da jinjinawa sojojin da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare kasa, tare da bukatar ‘yan Najeriya su sanya su a addu’a, da kuma kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su.

Maharan sun kashe sojoji 15 da ‘yan sanda 7 a harin kwantan-?auna da suka kai musu.

Kafin wannan lokacin sai da ‘yan ta’adda suka farwa wajen aikin hakar ma’adini na ‘yan China da ke Ajata-Aboki a yankin Gurmana da ke karamar hukumar Shiroro.

Cikin wadanda aka kashe a harin akwai ‘yan sanda bakwai da wasu sojoji.

Shiroro gari ne mai mutukar amfani ga Najeriya inda ake da tashar wutar lantarki da ke samar da megawatts 600.

Related posts

Leave a Comment