An ja hankalin jama’ar Najeriya musamman na yankin arewa, da cewar su mayar da al’amurra ga Allah sannan su dage ga yin addu’o’i na samun zaman lafiya a yankin Arewa,domin halin da muke ciki yanzu ya biyo bayan abin da muka shuka ne.
Mai martaba Sarkin Birnin Gwari Alhaji Zubairu Jibirin Mai Gwari na Biyu ya yi wannan jan hankali, a yayin da yake gabatar da gajeruwar hu?uba kafin zuwan Liman a babban Masallacin Juma’a na Sarkin Musulmi Bello da ke garin Kaduna.
Mai martaban ya ?ara da cewar, yankin Birnin Gwari yanki ne da ya dade yana fama da marsalar rashin tsaro tun daga kan garkuwa da mutane har ya zuwa satar shanu sama da shekaru 20, amma cikin ikon Allah jama’ar gari suka tashi tsaye wajen maganin matsalar, sai dai abin takaici shine abubuwa sun ?ara lalacewa ne bayan zuwan mulki na siyasa.
Zubairu mai Gwari ya cigaba da cewar, a yau a Najeriya musamman yankin Arewacin Najeriya abubuwa sun dagule, dukkanin abubuwan ba?ala da ba’a san dasu ba a baya, yanzu ana aikata su a yankin, Miyagun abubuwan kamar luwa?i da Ma?igo sun zama ruwan dare, da wannan ka?ai Allah zai iya azabtar da mu.
Daga karshe Sarkin na Birnin Gwari ya shawarci jama’a da komawa ga Allah tare da yi wa kawunan su hisabi kafin zuwan kamun Allah.
