Sulhu Ne Ka?ai Hanyar Magance Matsalar Tsaro -Farfesa Usman Yusuf

An bayyana cewar zaman sulhu a tsakanin gwamnati da wa?anda ake kira ‘yan bindiga ita ce hanya guda da ta saura wajen samar da tsaro a ?asa, inda aka bukaci shugabanni a yankin Arewa da su yi kokarin zama da wadannan ‘yan bindiga domin samun nasarar da ake nema.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin tsohon Shugaban Hukumar inshorar lafiya ta ?asa Farfesa Usman Aliyu lokacin da yake jawabi a cikin shirin”Ba?onmu Na Mako” da gidan Talabijin na Liberty Abuja ya yi dashi.

Farfesa Usman wanda yana ?aya daga cikin wa?anda suka rufawa Dr. Ahmad Gumi baya a ziyarar da ya kai dazukan Zamfara da Kebbi domin ganawa da ‘yan bindiga, yace ko ka?an matakin amfani da ?arfin Soji ba zai haifar da nasara ba sai dai ?ara dagula al’amurra.

“Abubuwan da na gani a ziyarar da muka kai wa ‘yan bindiga abu ne dake sanya damuwa, tabbas akwai ?orafin da suke yi na anyi watsi dasu da rashin nuna kulawa da halin da suke ciki, wanda hakan ya ke tunzura su suke ?aukar matakan ?watar kai”.

Farfesa Usman Aliyu ya tabbatar da cewar yana da kyakkyawan yakini muddin Gwamnati ta kusanci wa?annan ‘yan bindiga ta hanyar yin sulhu dasu tabbas za su mi?a makamansu da rungumar tsarin zaman lafiya. Inda ya nuna damuwar shi akan aniyar wasu gwamnoni musamman na yankin Arewa maso yammacin Najeriya da ke sukar matakin sulhu da ‘yan Bindigar da cewar su sake tunani.

Dangane da rikicin kabilanci da ya kunno kai a sashin Kudancin Najeriya musamman Jihohin Yarbawa dangane da kisa da korar Fulani da ake yi a yankin, Farfesa Usman ya gargadi shugabanni da yin gaggawar ?aukar mataki domin da?ile yiwuwar ballewar rikicin kabilanci a ?asar wanda zai haddasa zubar da jini da kisan ?are dangi, kamar yadda aka samu a kasashen Laberiya da Ruwanda.

Related posts

Leave a Comment