Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar ?an bindiga masu satar mutane sun nemi a ba su shinkafa maimakon ku?i domin su saki mutanen da suka yi garkuwa da su a jihar Sokoto, biyo bayan yadda matsaloli ke kara afka musu.
Wani mazauni garin Sabon Birni na jihar Sokoto ya shaida wa jaridar Dailytrust cewar ?an bindigar sun saki yarinyar makwabcinsa bayan an kai masu abinci.
Kuma rahotannin sun ce mudun shinkafa 10 aka kai wa ?an bindigar suka saki yarinyar.
Haka kuma kuma wasu ?an bindigar sun bu?aci akai masu buhun shinkafa da kwalayen taliya kafin su saki wani direban mota bayan da farko sun bu?aci a ba su miliyan 15.
An haramta cin kasuwanni a jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina da Kaduna da Neja, matakin da ake ganin ya jefa ?an fashin cikin yunwa.
