Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya bu?aci Rundunar Sojin Nijeriya, da ta sake yin dubi akan dabarun ya?in da take amfani dashi.
Tambuwal ya bayyana haka a lokacin da Babban Hafsan sojin Najeriya Laftanar-Janar Faru? Yahaya ya kai mashi ziyara, a gidan Gwamnatin jahar a ranar 18 ga watan Oktoba na shekarar 2021.
Wannan na ?unshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hul?a da jama’a Onyema Nwachukwu ya sanyawa hannu aka fitar dashi a ranar Litinin.Gwamna Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan yace harin da ?an ta’adda suka kai a ?auyen Goronyo abin ba?in ciki ne, a saboda haka akwai bu?atar dake akwai na sake yin dubi akan dabarun ya?i a shiyyar domin magance sake faruwar hakan.
“Ya kuma jaddada bu?atar dake akwai na ?an ?asa da jami’an tsaro dasu gano wa?anda suka aikata ta’addancin a cikin al’umma, inji sanarwar.
Ya kuma yi kira ga al’umma da kada su goyi bayan duk wani mai goyon ?an ta’adda, musamman masu sanar dasu bayanan sirri da ku?a?e.
Yayi kira ga Gwamnatin Tarayya data ?aro jami’an tsaro, domin baiwa hukumomin tsaro damar gudanar da ya?i cikin sau?i.
A jawabin shi, Babban Hafsan sojin Najeriya Laftanar-Janar Faru? Yahaya ya yabawa Tambuwal na irin cigaba da bayar da goyon bayan shi ga Rundunar sojin Najeriya, inda ya bu?ace shi daya cigaba da hakan.
Ya bada tabbacin cewa, Rundunar sojin Najeriya bazata baiwa gwamnati kunya ba, a ?o?arin ta na inganta ya?in da akeyi a yankin Arewa maso Yamma.
