Shugabancin Tinubu Rahama Ne Ga ‘Yan Najeriya – Shettima

Mataimakin Shugaban ?asa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa samuwar Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya, ba sa’a ko gam-da-katar ba ne, wata mu’ujiza ce daga Allah ma?aukakin Sarki.

Kashim ya ce Allah ya bai wa Najeriya shugaba mai tsarkakkar zuciya, shi ya sa ya zama shugaban ?asa.

Shettima ya bayyana haka ranar Juma’a, lokacin da ya kar?i ba?uncin tawagar shugabannin Hukumar Aikin Alhazai ta Kiristoci, wato NCPC, wa?anda suka kai masa ziyara a Fadar Shugaban ?asa, a Abuja.

“Dajin da muka keto har Shugaba Bola Tinubu ya samu nasara ba sa’a ba ce ka?ai ko wani gam-da-katar.

“Tinubu mutum ne da ya da?e ya na taka rawar ganin ciyar da ?asar nan gaba.

“Nasarar lashe za?en da Shugaba Tinubu ya samu, wata mu’ujiza ce daga Allah. Kuma sakayya ce Allah ya yi masa, saboda zuciyar sa tsarkaka ce,” inji Kashim Shettima.

Mataimakin Shugaban ?asa ya jaddada muhimmancin shugabanni wajen ?inke ?araka da gina gadar ha?e mabambanta wuri ?aya, domin hakan zai kawo zaman lafiya da ci gaban al’umma.

“To shi kuwa Shugaba Tinubu ya sadaukar da kan sa, kuma ya ?inke ?araka. Kuma ya kasance mutumin da aka ri?a yi wa bi-ta-?ullin siyasa, har Allah ya Allah ya sa ya zama Shugaban ?asa.

“Ko lokacin da sauran gwamnoni suka ri?a kai gwauro su na kai mari wajen tsohon Shugaban ?asa, Olusegun Obasanjo, shi kuwa Tinubu sai ya kafa jam’iyyar siyasa mai hangen nesa da tsinkaye,” inji Shettima.

Daga nan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da juriya da kuma bai wa Shugaba Tinubu uziri da lokaci, yayin da ya ke ?o?arin tattabar da samun nasarar fatattakar ?alubalen da ke addabar ?asar nan baki ?aya.

“Saboda shi dai Shugaba Tinubu ba wai tsautsayi ne ya kai shi mulkin ?asar nan, ko sa’a ko gam-da-katar ba. Shi mu’ujiza ce daga Allah.”

Daga nan ya yi kira ga sabbin shugabannin hukumar Alhazan Kiristoci ta Najeriya su ci gaba da jajircewar wajen yin aiki tu?uru.

Ya tunatar da shugabannin hukumar muhimmancin addini wajen shawo kan ?alubalen da ?asa ke fuskanta.

Tun da farko, Babban Sakataren NCPC, Stephen Adegbite, wanda babban limamin Majami’a ne, ya fara da godiya ga Shugaba Tinubu, saboda damar da ya ba su, domin yin aiki a hukumar.

Haka kuma ya yabi Mataimakin Shugaban ?asa, Kashim Shettima, bisa shugabanci nagari da ya yi a lokacin da ya na gwamnan Jihar Barno.

“Lokacin da muka je Maiduguri, ni ne Daraktan Al’amurran ?asa na ?ungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN).

“Shugaban CAN na Jihar Barno a lokacin, ya shaida mana irin irin ayyukan alherin da ka yi wajen goyon bayan Kiristocin Jihar Barno.

“Ka gina masu coci-cocin da Boko Haram suka rushe masu,” inji shi.

Ya ce Mataimakin Shugaban ?asa, Shettima, ya kasance ya na bai wa coci-coci goyon baya, kuma ya na tabbatar da an samu zaman lafiya da fahimtar juna a coci-cocin Najeriya da sauran mabiya wasu addinan a Najeriya.

Related posts

Leave a Comment