Wasu manyan masu fada aji a Najeriya sun yi ittifakin cewa Najeriya ta zama kamar mota maras matuki kuma duk mota mara mai juyata hadari za tayi.
Wadannan mutanen sun hada da babban faston katolikan, John Cardinal Onaiyekan; tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega; Dr Hakeem Baba Ahmed da Janar Martin Luther Agwai (mai murabus) Sauran sune Jibrin Ibrahim, Dr. Nguyan Shaku Feese, Dr. Usman Bugaje, Adagbo Onoja, Amb. Fatima Balla, Ambassador Zango Abdu, Auwal Musa Rafsanjani, da Chris Kwaja.
Hakazalika akwai Dr. Hussaini Abdu, Kemi Okenyodo, Jim Gala, Aisha Muhammed Oyebode da Tsema Yvonne Sun bayyana hakan a jawabin da suka saki ranar Alhamis karkashin kungiyar aiki domin samar da zaman lafiya da shugabanci (NWGPG).
Sun yi ikirarin cewa sune wadanda suke son ganin Najeriya ta gyaru. A cewarsu, Najeriya ba tada wani shugabanci na kwarai, kawai tuka kanta take yi.
“Sakamakon haka shine rashawan da ta wuce gona da iri, gashi kuma ana kokarin kashe hukumomin yaki da rashawan, yayinda aka rage gurfanar da barayi kuma suna kara yawa.”
Sun ce lokaci ya yi da ya kamata mutanen Najeriya su tashi tsaye, su daina korafi da surutai, su hada kansu. A cewarsu, rashin tsaro na karuwa kulli yaumin kuma babu wani takamammen shirin da ake yi na shawo kan matsalar .
Hakazalika sun yi gargadin cewa mutane sun fara fidda rai daga kasar nan kuma hakan ya sabbaba kiraye-kirayen ballewa da wasu sassa ke yi.
