Shugabancin Kasa: Ina Tare Da Tinubu Dari Bisa Dari – Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ?ara jaddada cikakken goyon bayansa 100 bisa 100 ga Bola Ahmed Tinubu, ?an takarar shugaban kasa a inuwar APC, a babban za?en dake tafe na shugaban kasa.

Buhari ya sanar da hakan ne a Jihar Gombe, Sanata Ahmad Lawan da wasu gwamnonin APC sun mamaye Gombe domin halartar rali da kuma kaddamar da kwamitin kamfen Tinubu/Shettima a jihar.

Shugaba Buhari ya bukaci mazauna jihar Gombe su zabi Bola Tinubu da sauran yan takarar jam’iyya mai mulki ta APC daga sama har ?asa.

Buhari, wanda ya samu wakilcin ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Farfesa Isa Pantami, ya ce ra?e-ra?in da ake ya?awa cewa ba ya goyon bayan Tinubu ba gaskiya bane.

Shugaban ?asan ya bayyana cewa zai ci gaba da aiki ba kama hannun yaro wajen tabbatar da nasarar Tinubu da kuma APC a babban za?en 25 ga watan Fabrairu.

Related posts

Leave a Comment