Shugaban ?asa Muhammadu Buhari ya ce zai ci gaba da yi wa ?an takarar jam’iyyarsu ta APC kamfe, Bola Ahmed Tinubu, don ya zama “shugaban ?asa na gaba”.
Da yake magana a gaban dubban magoya bayansu a Jihar Nasarawa ranar Asabar, Buhari ya ce ya yi imanin Tinubu zai sadaukar da kansa ga Najeriya wajen
“Kamar yadda Tinubu ya fa?a cikin jawabinsa, na san shi fiye da shekara 20, kuma zan ci gaba da taya shi ya?in neman za?e,” in ji Buhari cikin wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar.
“?an ?asa ne jajirtacce kuma na yi imanin zai sadaukar da kansa wajen yi wa Najeriya aiki.”
Kalaman nasa na zuwa ne kwana biyu bayan wasu jiga-jigai a APC sun yi zargin cewa wasu manya daga cikin jami’an gwamnatin ta Buhari na adawa da takarar Tinubu.
A cewar Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, masu adawar ba sa son APC ta yi nasara ne saboda ?an takarar da suka mara wa baya a za?en fitar da gwani bai yi nasara ba.
