Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnonin jam段yyar APC sun ce za su marawa duk wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya goyi baya a taron gangamin jam段yyar na kasa da za a gudanar a ranar Asabar 26 ga watan Maris.
Shugaban kwamitin tsare-tsare na jam段yyar APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya jagoranci gwamnonin zuwa wata ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa.
Shugaban kungiyar gwamnonin jam段yyar kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya shaida wa manema labarai bayan ganawar cewa za su goyi bayan duk wata hanya da za ta kai ga cimma matsaya wajen zaben shugabannin jam段yyar.
A watan da ya gabata ne shugaba Buhari ya ce yana goyon bayan tsarin da aka amince da shi na zaben 惣an takarar mukaman jam段yyar na kasa.
Ya bukaci gwamnonin da su hada kansu wajen tabbatar da tafiyar jam’iyyar yadda ya dace. Hakazalika, gwamnoni da shugaba Buhari sun tattauna kan yadda taron gangami zai kasance a ranar 26 ga watan Maris din nan.
Wadanda suka halarci ganawar sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, da gwamnoni 16; Kebbi, Filato, Kogi, Yobe, Ogun, Kaduna, Ekiti, Ebonyi, Imo, Neja, Jigawa, Kwara, Zamfara, Nasarawa, Borno, da Osun.
