Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya yi tir gami da Allah wadai da masu han?oron auren jinsi, inda ya bayyana cewa auren jinsi ba zai taba faruwa ba a karkashin mulkin sa har abada ba.
Ya fadi haka ne a wani taron coci da aka yi a Mampong ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairu cikin dinbin jama’a.
”Na fadi hakan a baya, kuma bari na sake jaddada cewa ba a karkashin Shugabancin Nana Akufo-Addo za a halatta auren jinsi a Ghana ba.
“Ba zai taba faruwa ba. Bari in maimaita; ba zai taba faruwa ba,” in ji shi cikin tsananin fushi.
Bayanin nasa ya biyo bayan rufe wani ofishin LGBTQ + wanda aka bude kwanan nan a Accra, babban birnin kasar ta Ghana.
Batun auren jinsi ya ?ara samun karfafuwa a duniya tun bayan lashe zabe da sabon Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi, inda gwamnatin sabon Shugaban ta fito ?arara ta nuna goyon bayan ta ga masu auren jinsi.
