Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da na?a sabbin manyan hafsoshin tsaron Najeriya da kwamandojin fadar shugaban ?asa.
Matakin na zuwa ne bayan sabon shugaban ya sanar da matakin sallamar hafsoshin da ke jagorantar rundunonin tsaron ?asar daga aiki nan take.
Wata sanarwa da Mista Willie Bassey, daraktan ya?a labarai a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar, ta bayyana Mallam Nuhu Riba?u a matsayin Mashawarcin shugaban ?asa kan harkar tsaro wato National Security Adviser.
An yi ta muhawara kwanan baya, lokacin da Tinubu ya sanar da sunan tsohon shugaban hukumar ya?i da cin hanci da rashawa EFCC a matsayin mai bai wa shugaban ?asa shawara na musamman kan harkar tsaro.
Da wannan sanarwa, Mallam Nuhu Riba?u dai zai gaji Manjo Janar Babagana Mongunu (mai ritaya).
Shugaban Najeriyar dai ya na?a Manjo Janar C.G Musa a matsayin babban hafsan tsaro, bayan sallamar Laftanal Janar Lucky Irabor.
Sai kuma Manjo Janar T. A Lagbaja a matsayin babban hafsan sojin ?asa na Najeriya, inda ya canji Laftanal Janar Faruk Yahaya.
Haka zalika, Rear Admiral E. A Ogalla ya zama babban hafsan sojin ruwa na Najeriya, inda ya maye gurbin Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo.
Akwai kuma Air Vice Marshal H.B Abubakar a matsayin sabon babban hafsan rundunar sojojin sama na ?asar, inda ya gaji Air Marshal Oladayo Amao.
?arin manyan jami’an tsaron har da DIG Kayode Egbetokun a matsayin Babban Sufeton ‘Yan sandan Najeriya, inda ya maye gurbin Usman Al?ali Baba.
Haka kuma sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya na?a Manjo Janar EPA Undiandeye a mu?amin babban hafsan tattara bayanan sirri na tsaro wato Defence Iintelligence.
Sauran na?e-na?en da Shugaba Tinubu ya amince da su, akwai Kanal Adebisi Onasanya a matsayin kwamandan bataliyar tsaron fadar shugaban ?asa.
Sai Laftanal Kanal Moshood Abiodun Yusuf, matsayin sabon kwamandan bataliyar tsaron fadar shugaban ?asa runduna ta 7 da ke Asokoro a birnin Abuja.
Haka zalika, an na?a Laftanal Kanal Auwalu Baba Inuwa, kwamandan bataliyar tsaron fadar shugaban ?asa, runduna ta 177 da ke jihar Nasarawa.
Tinubu ya kuma na?a Laftanal Kanal Mohammed J. Abdulkarim matsayin kwamandan bataliyar tsaron fadar shugaban ?asa, runduna ta 102, da ke Suleja a jihar Neja.
Yayin da Laftanal Kanal Olumide A. Akingbesote zai kar?i ragamar aiki a matsayin kwamandan bataliyar tsaron fadar shugaban ?asa, runduna ta 176 da ke Gwagwalada a Abuja.
?arin manyan jami’an sojojin tsaron fadar shugaban ?asa da Bola Tinubu ya amince da na?in su, har da Manjo Isa Farouk Audu a mu?amin kwamandan kula da dakarun atilare na fadar shugaban ?asa.
Sai Kaftin Kazeem Koyejo Hamzat a matsayin kwamandan dakarun soji masu tattara bayanan sirri a fadar shugaban ?asa.
Akwai kuma Manjo TS Adeola a matsayin kwamandan kula da makamai a fadar, yayin da Laftana A. Aminu zai kasance matsayin mai taimaka masa.
Sanarwar ta ce hafsoshin da sauran jami’an da aka na?a kan mu?aman, za su ci gaba da kasancewa a matsayinsu har zuwa lokacin da za a tabbatar da su kamar yadda tsarin mulkin Tarayyar Najeriya ya tanada.
