Tsohon Sanata mai wakiltar maza?ar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani, ya zayyano wasu abubuwa har 10 da duk wani dan Najeriya dake burin shiga siyasa zai shirya musu kafin ya tsunduma cikin siyasa.
A cewar tsohon Sanatan, jerin abubuwa 10 shawara ce ga duk wani mutum da ya bu?atar sanin manhajin siyasa kafin ya tsunduma siyasa.
Ga su kamar haka:
- Kashewa shugabannin jam’iyya ku?i domin samun tikitin takara duk da cewa babu tabbacin za su za?e ka. Amsa kira, halartar kowanne taron jama’a, sakarwa ‘yan jagaliya mara da hakuri da wautarsu.
- Takura, rashin samun lokacin kanka da na iyalanka sakamakon taro da jama’a koyaushe, ?o?arin ha?uwa da mutane da boyewa wasu mutanen.
- Dole ka koyi kawar da kai daga zagi daga mutanen da kake ganin kafi ko sun fika ta kafafen watsa labaran na radiyo, itv da sauransu.
- Abokan hamayyarka za su bi diddigin rayuwarka ta baya da tarihin iyayenka don samo abin suka, idan babu su kirkiro wanda za su gayawa jama’a ba. Idan ke mace ce ki shiryawa zagi kala-kala daga mazan da kika sani da wa?anda ma ba ki ta?a saninsu ba.
- Idan namiji ne kai to addininka da asalin kakanninka duk sai an bibiya. Har makarantun da ka yi za su bi don jin mummunan halinka, in suka samu tarihin rashin lafiyarka ko mutuwar auren ka, za su ya?ata ga jama’a.
- Ka shiryawa masu yaudara da son ta?e ka daga mutanen da kake son su, kila ma ka goyi bayansu ko ka taimakesu a wani abu.
- Ka shiryawa shiga cin bashi don gudanar da ya?in neman za?e, uwa uba sayar da kadarorinka da hannun jarinka wanda ka tara tsawon lokaci a rayuwarka, duk din ka tabbatar kana da ku?i don tafiyar ta yi kyau.
- Ka zama cikin shirin jin mutumin da ya ce zai taimake ka da rana ka hango shi a taron abokan hamayyarka da dare suna mitin. Ka shirya kamar ka yarda da abinda ya fada koda karya yake 9. Ka dai shiryawa shiga damuwa da tursasawa ?wa?walwaka, zuciya da gangar jikinka fiye da ka’ida. Ka zauna cikin shirin jin labarai na yi maka zagon-?asa, barazana da rayuwarka da ta iyalanka.
- Ka shirya bin hanya mai tsaurin gaske.
