Rahotannin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa mafi alheri shine a sasanta tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya wajen kotu, kan batun shari’ar wanda ke da ha??in kar?ar Harajin Jiki Magayi, wato ‘VAT’, wadda ake gwabzawa a kotu.
Idan ba a manta ba, Babbar Kotun Tarayya ta Jihar Ribas da ke Fatakwal ce ta fara bai wa Jihar Ribas iznin cewa ita ke da ikon kar?ar Harajin ‘VAT’ a Ribas, ba Gwamnatin Tarayya ba.
Tun daga lokacin kuwa Gwamna Wike ya hana Gwamnatin Tarayya kar?a a jihar sa. Kuma ya kafa sabuwar doka.
Ganin haka, ita ma gwamnatin Jihar Legas ta bi sahun Ribas ta fito da dokar da Majalisar Jihar ta amince da ita cewa ita za ta ri?a kar?ar ‘VAT’ a Legas ba tarayya ba.
Su ma ?ungiyar Gwamnonin Kudu kaf sun goyi bayan Legas da Ribas, cewa jihohi ke da ikon kar?ar VAT ba tarayya ba.
Cukumur?ar dai ta samo asali ne ganin yadda ake kwasar ku?a?en VAT da gwamnatin tarayya ke kar?a a jihohin da aka fi tara ku?a?en shiga, ana gabza wa wasu jihohin Arewa, wa?anda ba su iya tara harajin komai a jihohin su.
A ranar 10 Ga Satumba, Manyan Al?alan Kotun ?aukaka ?ara su uku, a ?ar?ashin Haruna Tsammani suka umarci ?angarorin jihar Legas da Ribas da kuma Tarayya cewa kowa ya maida takobin sa cikin kube, su jira hukuncin da za su zartas.
Ita kuwa Ministar Harkokin Ku?a?e, Zainab Ahmed cewa ta yi mafi alheri shi ne a yi amfani da teburin siyasa a sasanta a wajen kotu.
“Domin idan aka ce a kotu za a yi ta ta ?are, to za a ?auki tsawon lokacin ana gwabza shari’a.”
Musabbabin Rikicin ‘VAT’ Tsakanin Gwamnatin Tarayya Da Jihohi:
Yadda Kotun Tarayya ta bai wa Gwamna Wike iznin
kar?ar harajin VAT, ba da son ran Gwamnatin Tarayya ba:
Rikici ya tirni?e tsakanin Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Ribas, bayan da Babbar Kotun Tarayya da ke Fatakwal ta kwace ikon kar?ar harajin ‘VAT’ a Jihar Ribas daga hannun Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS), ta dan?a wa gwamnatin jihar.
Lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis 19 Ga Agusta, 2021, ya sa nan da nan Gwamna Nysom Wike ya rattaba hannu a kan dokar da Jihar Jihar za ta fara kar?ar harajin VAT a jihar, kuma ta hana a ri?a bai wa Gwamnatin Tarayya wannan haraji ta hannun FIRS.
Ba a nan dambarwar ta tsaya ba, haka kuma Babbar Kotun Tarayya ?in ta yanke hukuncin cewa Gwamnatin Jihar Ribas ce ke da ikon kar?ar duk wani haraji a jihar, ba Gwamnantin Tarayya ba.
Wanann hukunci dai kenan ya na nufin kowace jiha za ta iya amfani da wannan hukunci ta ri?a kar?ar harajin VAT ta na zubawa aljihun ta kenan.
Kuma hukuncin na nufin an hana Gwamnatin Tarayya kar?ar ku?a?en haraji a jihohi.
FIRS Ta ?aukaka ?ara:
Hukumar Tara Ku?a?en Shiga ta Tarayya (FIRS) ta ?aukaka ?ara dangane da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Fatakwal ta yanke, inda ta haramta wa hukumar kar?ar harajin VAT a jihar Ribas.
Haka nan kuma wata sanarwa da ta fito daga Babban Jami’in Ya?a Labarai na FIRS, Abdullahi Ahmad, ya yi kira da kada a bai wa Gwamnatin Jihar Ribas Harajin VAT, a ri?a bai wa Gwamnatin Tarayya, ta hannun FIRS kamar yadda aka saba.
Wannan dambarwa ta faru daidai makon da Najeriya ta sha alwashin tara harajin naira tiriliyan 10.1 cikin 2022.
Gwamnatin Tarayya ta ?udiri aniyar tara naira tiriliyan 10.1 na ku?a?en harajin cikin gida a cikin 2022.
Shugaban Hukumar Tara Ku?a?en Haraji ta ?asa (FIRS), Mohammed Nami ne ya bayyana haka.
Nami ya yi wannan alwashin a ranar Laraba, lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitin Harkokin Ku?a?e na Majalisar Tarayya, a Abuja.
Ya ce hukumar sa tuni ta tsara wani tsarin da zai tabbatar an tara wa?annan ma?udan ku?a?en cikin 2022.
Nami ya ce za a tara ku?a?en ne daga ku?a?en harajin da Najeriya ke samu baki ?aya.
Da ya ke na sa jawabi, Shugaban Kwamitin Harkokin Ku?a?e a Majalisar Tarayya, James Dake, ya jinjina wa Shugaban Hukumar FIRS ?in, kuma ya ?ara masa ?warin guiwar ganin cewa an samu wa?annan ma?udan ku?a?en da hukumar ta sha alwashin ta tara a cikin shekara mai zuwa.
