Assalamu alaikum barkanmu da asubahin lahadi, biyu ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin ga watan Satumba, shekarar dubu biyu da ashirin.
- A jiya hankali ya fi karkata ga zaben gwamnan jihar Edo da aka yi. A yanzun haka ana can ana ci gaba da hada hancin alkaluman sakamakon zaben. Gwamna Obaseki da ke yin takara a jam’iyyar PDP da na APC Ize Iyamu duk sun kada tasu kuri’ar a mazabunsu. Sai dai an ta korafin ba a kiyaye da ka’idojin kauce wa yada ko daukar cutar kwaronabairos ba. Zaben ya gudana lafiya sai wata mazaba da aka ce an yi harbi. An ce a lokacin hada hancin alkaluman ne, nan rikici kan tashi. Zuwa yanzun ba a ji komai ba tukuna.
- Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba hanya. Wata da watanni ba wuta. Ga tsadar taki ga ambaliya. Ga gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzu, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe. In sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
- Wasu malaman jami’o’i da sauran ma’aikata na wasu jami’o’i na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin wata na hudu ke nan ba albashi. Haka nan ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin iimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.
- Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos 189 a jihohi da alkaluma kamar haka:
Legas 70
Filato 37
Abuja 24
Kaduna 19
Ribas 12
Oyo 5
Ogun 4
Ebonyi 3
Katsina 3
Ondo 3
Oshun 3
Imo 2
Yobe 2
Ekiti 1
Nasarawa 1
Jimillar da suka harbu 57,145
Jimillar da suka warke 48 431
Jimillar da ke jinya 7,619
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,095
- A gobe litini ashirin da daya ga watan nan Gwamnatin Tarayya za ta bude dandalin nan na intanet da kananan ‘yan kasuwa da matsakaita da sauran marasa karfi, za su leka don cikewa, don samun kaso daga cikin wata naira biliyan saba’in da biyar da gwamnati za ta raba.
Mu wayi gari lafiya.
Af! A duk lokacin da nake fassara labarun da zan karanta a rediyo ko talabijin nakan yi taka-tsan-tsan idan na zo wajen labarun da gwamna ke da mata biyu ko uku ko hudu in rasa wacce ce uwargida. Misali jiya ni na fassara labarun almuru na gidan rediyon alheri da talabijin na DITV da ke Kaduna. Akwai labarin Ummi El-Rufai a kan batun yaki da fyade da cin zarafin mata da yara. A labarun turancin cewa aka yi THE WIFE OF THE GOVERNOR UMMI EL-RUFA’I. To akwai masu ra’ayin cewa in kana labaru bai kamata ka ce MATAR GWAMNA BA, sai dai ka ce UWARGIDAR GWAMNA. To mu dauka UMMI ba ita ba ce uwargidar gwamna El-Rufai, ita ce ce ta biyu ko ta uku. Amma ita ce kake labaru a kanta. Sai kai mai labaru ko fassara a rediyo ko talabijin ko jarida ka ce UWARGIDAR GWAMNA EL-RUFAI HAJIYA UMMI. Sai ainihin uwargidar tasa ta ga labarun ko ta ji ko ta karanta a jarida. Anya Uwargidar ba za ta ji haushi ba kuwa? Wasu sun kawo shawarar a dinga cewa MAI DAKIN GWAMNA. To in su biyu ko uku ko hudun ne fa? Anya sauran musamman ta farkon ko ta biyun ko ta ukun ba za su shaka ba kuwa idan amaryar ce kai mai labaru ka kirata da mai dakin gwamna?
Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :
https://www.facebook.com/2356865571252507/posts/2707546809517713/
Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.
