Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Gui?i

Assalama alaikum barkanu da asubahin juma’atu babbar rana, goma sha biyar ga watan Muharram, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da hudu ga watan Satumba, shekarar dubu biyu da ashirin.

  1. A daren juma’a akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su 125 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 42
Abuja 25
Katsina 14
Kaduna 11
Kwara 8
Ondo 7
Delta 4
Anambara 3
Oyo 3
Edo 2
Ogun 2
Oshun 2
Kuros Ribas 1

Jimillar da suka harbu 54,588
Jimillar da suka warke 42,677
Jimillar da ke jinya 10,863
Jomillar da suka riga mu gidan gaskuya 1,048

  1. ‘Yan bindiga sun kai hari wurare daban-daban na jihar Neja har sun kashe kusan mutum ashirin da ‘yan JTF, sai dai su ma ‘yan bindigan an kashe su da dama.
  2. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce bai ji dadin yadda kayan abinci suka yi wa talaka tsada ba, tare da bai wa ‘yan Nijeriya hakuri.
  3. Sojoji sun kashe wasu ‘yan bindiga su hudu a Kaduna, da kwato makamai.
  4. Malaman kwalejojin ilimi da aka fi sani da COEASU, za su tafi yajin aiki na kasa baki daya. Da ma malaman jami’a sun ce ba za su koma aiki ba. Su kuwa na kwalejojin foliteknik korafi suke ci gaba da yi cewa shekara daya da wata shida ke nan suna zaman jiran ariyas na sabon albashi.
  5. Za a sake bude sansanoni na horas da ‘yan bautar kasa a lokacin da aka sake bude makarantu da ke kulle saboda kwaronabairos.
  6. An amince silma da wuraren shakatawa su dan bude bayan kulle su saboda kwaronabairos.
  7. Atiku Abubakar ya ce bai dace a yi karin kudin wutar lantarki a wannan yanayi da ake ciki ba.
  8. Maina ya rubuta wa babban lauyan gwamnatin tarayya wata bukata ta a sake duba tuhume-tuhumen da ake masa na zargin damfara.
  9. Karamin ministan mai Timipre ya kare karin kudin fetur da aka yi, da bai wa masu ababen hawa da sauran jama’a da ke amfani da fetur, shawarar su kyale fetur su koma amfani da man gas ya fi sauki. Ya ce gwamnati ba za ta ci gaba da kashe naira tiriliyan daya a kan tallafin kudin mai ba.
  10. Gwamnatin tarayya ta ba da umarnin fitar da masara tan dubu biyar don tallafa wa masu kiwon kaji da danginsu da suka soma korafin masarar ta yi tsada.
  11. Talakan Nijeriya na nan yana ci gaba da korafin tsadar rayuwa, ga tsadar shinkafa, da masara da dawa da sauran hatsi, ga tsadar sauran abin masarufi, ga karin kudin wuta da na fetur.
  12. Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna na can suna ci gaba da kasancewa a killace, shekara da shekaru ba hanya, wata da watanni ba wutar lantarki, ga tsadar taki, ga gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe cewa idan suka zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
  13. A nemi jaridar Leadership Hausa A Yau Juma’a don karanta shafukana da ke dauke da rubutun labarun da na kawo muku daga juma’ar da ta gabata zuwa jiya alhamis.

Mu wayi gari lafiya, mu yi juma’a lafiya.

Af! Wai ina batun Keyamo da ‘yan majalisa, da batun Akpabio da ‘yan majalisa ne? Ko dama duk bula ce da wasa da hankalin talakan Nijeriya?

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://www.facebook.com/2356865571252507/posts/2693776460894748/

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Related posts

Leave a Comment