Sharhin Bayan Labarai: Daga Ishaq Idris Gui?i

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin Laraba ta Bawa ranar samu, ashirin da biyar ga watan Rabi’ul Awwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da goma sha daya ga watan Nuwamba, na shekarar 2020.

  1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani tsari na tallafa wa matasa manoma.
  2. Mataimakiyar Shugaban Majalisae Dinkin Duniya Amina Mohammad, ta gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da alkawarin Majalisar za ta tallafa wa wasu kasashe har da Nijeriya, su samu su farfado daga halin da suka shiga na durkushewar tattalin arziki sakamakon kwaronabairos. Ta ce wannan durkushewa ce ta sa matasa zanga-zanga a duniya.
  3. Gamaiyyar Kungiyoyin Matasan Arewa, ta nemi Majalisar Dinkin Duniya ta haramta kungiyar nan ta IPOP musamman idan aka yi la’akari da rawar da ta taka ta hanyoyi daban-daban a zanga-zangar #ENDSARS da ta rikide har da kashe-kashe na kabilanci.
  4. Sojoji na sama, sun kashe ‘yan ISWAP da lalata wurarensu a jihar Barno. Sojojin sun kuma gyara jiragen yaki samfurin Fighter Jet F-7 har guda 9, sai kuma wasu sabbi guda uku daga Pakistan.
  5. Gwamnan jihar Legas Sanwo-Olu ya yunkura don soke fanshon da ake biyan tsofaffin gwamnoni da mataimakansu na jihar.
  6. Kotu a Dubai ta yanke wa wasu mutum shida hukunci daban-daban har da daurin-rai-da-rai, saboda gano su suna tallafa wa kungiyar Boko Haram gudanar da aikace-aikacenta a Nijeriya daga can.
  7. Ana ci gaba da zargin juna, tsakanin kungiyoyin malamai da na sauran ma’aikatan jami’o’i manyansu da kanana, a bangare guda, da kuma Gwamnatin Tarayya a ta daya bangaren, wane ne ke kokarin durkusar da karatun jami’a a Nijeriya?
  8. Yau arba’in da daya ga watan Oktoba, ga yawancin ma’aikatan kwalejojin foliteknik, saboda yau goma sha daya ga watan Nuwamba, ba albashin Oktoba, babu dalilinsa. Kuma suna korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi. Ariyas din da suke zargin an fi shekara da biyan sauran ma’aikata da ke wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati.
  9. Akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos mutum 152 a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 93
Abuja 21
Oyo 15
Ribas 11
Bauci 7
Kwara 2
Bayelsa 1
Edo 1
Filato 1

Yau sun manta ba su ba Kaduna ba. Ba mamaki gobe ta shige gaban kowacce jiha da nata alkaluman. Yahaya Bello na Kogi dai ya ‘yanta jiharsa ba ruwansu da kwarona.

Jimillar da suka harbu a Nijeriya 64,336
Jimillar da suka warke 60,333
Jimillar da ke jinya, 2,843
Jimillar da suka riga mu gidan gaskiya 1,160

  1. Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna musu alkawarin hanya har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura, ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa ba gyara musu ba.

Mu wayi gari lafiya.

Af! Allah Ya yi wa Dan Iyan Zazzau, Hakimin Kabala Alhaji Yusuf Ladan rasuwa, kuma jiya aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanadar. Uba a aikin rediyo da talabijin. Daya daga cikin wasannin kwaikwayo da yake rubutawa a lokacin da yake aiki da RTK aka mayar da shi littafi, shi ne ZAMAN DUNIYA IYAWA NE da ake amfani da shi wajen koyar da dalibai a mataki daban-daban. Bayan mukamai da ya rike a Rediyon Nijeriya na Kaduna, ya kuma rike rediyon jihar Kaduna. Da ya ji kana karanta labaru ka ce RAWAR DA SARAKUNA ZA SU TAKA ko SUKE TAKAWA, zai sa a kira ka ofishinsa, ya tambayeka ka taba ganin sarkin garinku na tika ko taka rawa?
A lokacin da na fara gabatar da shirin MADUBI a tashar talabijin ta jihar Kaduna KSTV a wuraren shekararun 2000, nakan yawan gayyatarsa shirin, ya fede mana wasu kalmomi na Hausa. A wajensa na san cewa kalmar DURBAR asalinta kalma ce ta Hindu wato Indiyanci. Haka nan EMIR daga Larabci AMIR da sauransu.
A yanzun haka ma sunansa ne aka rada wa ginin rediyo da talabijin na KSMC da ke titin Wurno daura da titin Rabah da ke Badarawa Kaduna.

Allah Ya jikan Alhaji Yusuf Ladan, Ya sa mu da muka yi saura, mu cika da kyau da imani Amin.

Za a iya leka rubutun na yau a Taskar Guibi da ke DCL Hausa a :

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=2754464548159272&id=2356865571252507

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

Related posts

Leave a Comment